Daga Abubakar Abba,
A yanzu haka, Nijeriya ta kasance kan gaba wajen yawan masana’antun da ke sarrafa rake a nahiyar Afirka, inda kasar ke da kasar naomansa da za a iya noma rake a kalla tan miliyana biyar.
Fannin nomansa ba sai an zuba wani jari mai yawa ba domin za ka iya shiga fannin da naira dubu dari, inda kuma a kadada daya, za ka iya samun daga tan 80 zuwa tan 140.
Ingantaccen raken da za ka iya samu, ya danganta ne da yanayi mai kyau tare da kuma ba shi kulawar da dace, haka za ka iya ciwo bashi daga banki don yin noman.
Abubuwan Da Suka Kamata Ka Sani Kafin Shiga Fannin:
Samun kasar yin nomansa, sannan kuma ka yi masa gyara kafin ka fara yin noman na rake.
Hada-hadar Kasuwancinsa:
Yana da mahimmanci ka san kasuwar da ta dace ka kai rake da ka noma don sayar da shi, musamman kasuwar da ka san ana da matukar bukatarsa don ka samu riba mai yawa.
Daukar Ma’aikata: Yana da kyau ka dauko hayar ‘yan kwadagon da za su yi maka aiki a gonar taka da ka shuka raken, amma idan kasuwancin ya kara bunkasa akwai bukatar ka kara yawan ma’aikatan.
Yadda Tsarin Dasa Shi Yake A Gona:
Ana dasa shi ne a jere ko kuma a karkace, inda za ka dasa tushesa daga 12,000 kowace kadadarsa.
Kare Shi Daga Harbin Kwari Ko Cututtuka:
Ana bukatar manominsa ya tabbatar da ba shi kariyar da ta dace daga harbin kwari ko kuma cututtun noma, musamman masu lalata Jijiyoyinsa.
Sare Shi:
Wajen sare shi akwai matukar wuya, saboda haka, ana bukatar manominsa ya tatabbatar ya kiyaye sosai wajen sare shi, ana kuma sare shi ne, daga wata takwas zuwa goma sha biyu.
Haka kuma, ana sare shi daga watan Yuni zuwa na Disamba, musamman lokacin da ruwan sama ya ragu.
Bayan an sare shi, gonar da aka yi nomansa ana daina amfani da ita har zuwa tsawon wani lokaci, sannan kuma a yi wa kasar haro don gonar ta kara samun danshi yadda idan an zo shuka wani rake irinsa zai shiga cikin kasar naoma sosai.
Bugu da kari, manominsa zai iya yin nomansa har sau biyu a shekara daya.
Sayar Da Raken Da Aka Noma:
Kashi 90 daga cikin kasha dari na raken da ake noma wa a kasar nan, masana’antu ne suke saye don sarrafa shi zuwa wasu nau’uka daban-daban kuma ana samun kasuwanin da ake sayar da shi da dama a kasar nan za ka kuma iya kai shi kasar waje don sayarwa.