Zabo Gonar Data Dace: Ana bukatar wanda zai fara yin noman Waken Soya ya tabbatar da ya samu kasar noman da ta da ce haka bincike ya nuna cewa, yankunan Kudu Maso Babas da kuma Kudu Maso Yammacin Nijreiya sun fi kasar noman Waken Soya mai kyau.
Yana da mahimmanci a sani cewa, Irin Waken Soyar da aka shuka a lokacin ruwan damina ba kasafai ake samun amfani mai kyau ba, musamman saboda a wannan lokacin, akwai danshi a kas sosai, inda hakan zai iya yiwa Irin da aka shuka illa tun kafin ya fara girma.
Buhu Nawa Ake Samu A Kada Daya? Za a iya yin amfani da buhun takin zamani biyu ma su nauyin kilogiram 50 ako wacce kadada daya.
Nawa Ne Farashin Waken Soya A Nijeriya? Tan din Waken Soya na dauke da kilogiram dari na buhu daya, ya kai daga naira 135,000 zuwa naira 200,000 ya danganta da inda aka yiu nomansa.
Zabo Ingantaccen Iri: Akwai dubban Irin Waken Soya, amma yana da kyau ka zabo wanda yafi da ce wa, akwai Irin Waken Soyar da ake shuka wa domin ci kadai,da kuma wanda ake shuka wa don sarrafa amfanin zuwa wasu nau’kan abinci, Irin nau’kan Waken Soya da aka fi sani a Nijeriya sune, TGD 1448- 2E, TGD 1485-ID da kuma TGD 1835- 10E har Ila yau, iya adadin da ake bukata na shukar Irin Waken Soya a kadada daya akasari an kiysata ya kai daga kilogiram 50 zuwa kilogiram 60.
Yin Shuka A Kan Lokaci: Idan aka shuka Iein Waken Soya a watan Mayu zuwa watan Yuni katananfi samun amfani mai kyau kuma mai yawa haka ya fi dace wa ayi shukar a lokacin da kasar noman ta kai ma’aunin yanayi 60 F (15.5 C) ko kuma kimanin ma’aunin yanayin da ya kai kimanin 70(21 C), inda kuma ake fara yin girbi daga watan Okutoba zuwa watan Nuwamba ya danganta da lokacin da aka yi shukar.
Sinadaran, musamman don ya girma da wuri, domin idan kasar noman ba ta irin wadanan sinadaran, amfanin ya kan jima bai girma ba ana kuma bukatar manominsa ya kara zuba takin zamani don kasar noman ta kara inganci, haka manomi zai kuma iya kara zuba takin gargajiya.
Ana son a shuka irin ya kai inchi 1.5 ko kuma santi mita 3.8, inda kuma ake son a bayar da tazarar da ta kai santi mita 7.6.
Yin Ban Ruwa: Waken Soya na da bukatar a yi masa ban ruwa ana kuma son ayi ban ruwan a mataki uku, inda a tsakanin wannan lokacin, ake son a tabbatar da an yi masa ban ruwa sosai.