Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Matakin Da Amurka Ta Dauka Kan Tiktok Ba Zai Yi Mata Kyau Ba

Published

on

A kwanakin baya ne gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa, za ta dauki mataki kan manhajar TikTok ta kasar Sin da ake amfani da ita a ketare, lamarin da ya jawo hankalin al’ummun kasa da kasa. A jiya Litinin shugaban Amurka ya kara yin kashedin cewa, “Dole ne a sayar da manhajar TikTok ga kasar ta Amurka kafin ranar 15 ga watan Satumban dake tafe, in ba haka ba dole ne a daina yin amfani da ita”, kana ya kara da cewa, dole ne a gabatar da kudin da aka sayar da manhajar ga gwamnatin kasar Amurka. Tsokacinsa dake nuna fin karfi ya gamu da suka da shakku daga jama’a a cikin gida da wajen Amurka da sauran kasashen duniya.

Kwanan baya tsohon babban mai ba da shawara kan dokoki na ma’aikatar shari’a ta kasar Amurka Gene Kimmelman ya yi nuni da cewa, kalaman shugaban Amurka ba su da tushen doka a Amurka, kana wasu masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun nuna cewa, matakin da aka dauka matsin lambar siyasa ne da ‘yan siyasar Amurka da wasu shugabannin manyan kamfanonin yanar gizo suka yi cikin hadin gwiwa, lamarin da ya nuna adawar da ‘yan siyasar Amurka suke nunawa ga kasar Sin, kuma hakan na nuna cewa, babu adalcin yin takara a kasar ta Amurka.
Hakika tun tuni Amurka ta riga ta mai da hankali kan wannan manhaja wadda ke samun karbuwa matuka a kasashen yamma, amma akwai wahala ta samu fakewar daukar mataki kan ta, yanzu haka ta dauki mataki kan manhajar bisa fakewa da batun tsaron kasa, hakika wannan rashin kunya ne.
Ban da haka, an lura cewa, Amurka ta dauki wannan mataki ne domin wannan manhajar kasar Sin ta fi kamfanonin Amurka samun karbuwa a wajen masu amfani da yanar gizo na kasashen yamma, a don haka, take cikin zulumi har tana son hana a yi amfani da ita.
Hakika matakin Amurka ya sabawa ka’idar adalci ba tare da rufa rufa ba ta hukumar cinikayya ta duniya, sannan ba ta jin tsoron hana sauran kamfanonin ketare su shiga kasuwar Amurka a nan gaba saboda kila za su yi fama da irin wannan matsala da TikTok ta fuskanta, to idan masu kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha sun ki shiga kasuwar Amurka, ta yaya Amurka za ta samu ci gaba?(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai