Ibrahim Muhammad" />

Matakin Kare Yaduwar Covid-19 Ne Kadai Zai Dakile Ta – Dr. Getso

Shugaban Kwalejin kimiyyar Lafiya da Fasaha ta jihar Kano, Dakta Bashir Bala Getso ya bayyana cewa cutar nan mai sarke numfashi da aka kira Coroabirus ta samo asali ne daga haduwar wasu kwayoyin cututtuka masu raunana garkuwar Jikin dan’adam.

Dakta Bashir Bala wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Kano ya yi nuni da cewa cutar na faraway ne da alamomi da suka hada da mura da sarkewar numfashi. Sannan kuma idan har kwayar cutar ta fita daga cikin jikin dan’dam takan kwashe mintuna 30 kafin ta mutu.
Dakta Bashir Bala Getso ya ce, akwai abinda ake cewa” Incubation Period ” Lokacin kyankyasa kwayar cutar suna shiga jikin dan adam sukan dauki kwanaki 14 akalla shi ne karancin kwanaki kafin su fara nuna alamun cewa mutum yana dauke da wannan cuta.
Ya ce, su kwayoyin cuta idan ana so su rayu irin na wannan biros din idan ya kasance a waje ne yawancinsu cikin minti 30 za su iya mutuwa. Amma idan har yanayin bata basu damar su rayunba kenan. Duk lokacin da mutum yazo ya tabasu za su iya zama suna da rai ya kasance ya kamu da cutar.
Dakta Bashir Bala ya ce, fatansu shi ne jama’a su kiyaye da kula da tsaftar kansu dana muhallinsu. Kuma cutar bata numfashi ake daukarta ba tana kama dan’adam ta hanyar taba wasu sassan jiki da hannu dake dauke da kwayoyin cutar.
Ya ce, ita cuta ce da take dauke da yanayi wanda idan mutum ya yi tari yana dauke da wannan cuta idan ta shiga cikin wani abin shi kuma dan’adam yaje ya tabata zai iya samun dammar da shi kuma zai iya kaiwa jikinsa ta hanyar taba idonsa ko wasu kafofi na jikinsa wanda daga nan za ta iya shiga jikinsa ta haifar da matsaloli wanda suke da alaka da mura irinsu tari, zazzabi da shi kanshi atishawa ko numfashi yakan dauke daga nan mutum zai iya shiga yanayi na galabaita.
Dakta Bashir ya kuma ce, abinda yasa ake alakanta daukarsa ta numfashi shine idan mutum ya yi kaki ya tofar kamar numfashi ne. An yi tari mutum ya je ya taba shi kuma yaje ya kai bakinsa koya kai shi ido ko hanci tanan suke samun shiga jikin dan’adam su haifar da cutar.
Dakta Bashir Bala Getso ya ce, daukar matakai na kare yaduwar cutarne kadai zai taimaka wajen dakileta, kamar yanda aka gani ana yi a kasashen duniya.

Exit mobile version