CRI Hausa" />

Matakin Sin Na Dakatar Da Kafar BBC Ya Hallata

Ofishin jakadancin Sin dake Birtaniya, ya ce matakin hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasar Sin na dakatar da kafar yada labarai ta BBC daga watsa shirye-shiryenta a kasar saboda keta muhimman ka’idoji, halaltacce ne kuma bisa hujja.

A cewar kakakin ofishin jakadancin, dagewar BBC na yada karairayi dangane da kasar Sin, ya keta ka’idojin aikin jarida, kuma ya nuna fuska biyu da bangaranci da kuma harzuka al’ummar Sinawa.
Ya ce ikirarin ‘yancin yada labarai ba wani abu ba ne, face fakewa wajen yada labaran bogi da sukar kasashe, yana mai cewa dukkan kasashe na sa ido kan hukumomin yada labarai, kuma matakin hukumar ta kasar Sin halaltacce ne.
Kakakin ya yi kira da kafar BBC ta yi watsi da ra’ayin cacar baka, ta daina shiryawa da yada labaran bogi, da nuna bangaranci da rashin adalci, da suka da kuma shafawa JKS da ma gwamnatin kasar bakin fenti, ta dauki ingantattun matakan kawar da mummunan tasirin rahotanninta. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)

Exit mobile version