Daga Nasir S. Gwangwazo,
A karkashin Shirin Bada Tallafin Kudi ga Matan Karkara da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ke aiwatarwa, akalla mata 8,000 ne za su amfana a kananan hukumomi 44 da ke Jihar Kano.
Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ita ce ta bayyana haka a wajen bikin kaddamar da shirin wanda aka yi a Kano a ranar Litinin.
A yayin da ta ke magana ta bakin Babban Sakataren ma’aikatar, Bashir Nura Alkali, wanda ya wakilce ta a bikin, ministar ta bayyana cewa an fito da shirin ne a cikin 2020 domin a fadada shirin gwamnatin Shugaba Buhari na rage wa talakawa matsalolin rayuwa.
Ta ce: “An tsara shi ne domin a samar da tallafi biya daya ga matan da su ka fi kowa fatara da matsalolin rayuwa a yankunan karkara da gefen birane na kasar nan.
“Za a bada tallafin tsabar kudi N20,000 ga kowace a cikin kimanin mata fakirai guda 125,000 a dukkan jihohi 36 na kasar nan da Yankin Babban Birnin Tarayya.”
Ministar ta kara da cewa ana sa ran tallafin zai kara wa wadanda aka ba hanyoyin samun kudin shiga.
Hajiya Sadiya ta yi kira ga wadanda su ka amfana da shirin da su yi amfani da kudin wajen bada gudunmawa ga inganta rayuwar su ta yau da kullum.
Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a jawabin sa, ya yaba wa gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari saboda fito da shirye-shirye da ta yi don daga rayuwar jama’a da rage masu wahalhalun rayuwa, musamman mata da kananan yara.
Ya jinjina wa ma’aikatar saboda damar da ta ba Jihar Kano don matan karkara na jihar.
A karkashin shirin Bada Tallafin Kudi ta hanyar Tiransifa kuwa, wato Conditional Cash Transfer (CCT), gwamnan ya ji dadin yadda aka kara dibar mata guda 35,000 daga kananan hukumomi 15 na jihar, sannan ya yi kira ga ministar da ta amince a dauki ragowar mata 35,000 daga wadannan kananan hukumomin.
Ganduje, wanda Mataimakin Gwamna, Dakta Yusuf Nasiru Gawuna, ya wakilta a bikin, ya bukaci a fadada Rajistar Jama’a ta jihar don a hada da sauran kananan hukumomi 29 na jihar wadanda su ka rage, da kuma karin sauran shirye-shiryen bada lamuni (irin su Trader Moni, Market Moni da Farmer Moni) a zagaye na gaba na shirin, da sauran su.
A wani labarin makamancin wannan, an bayyana cewa sama da mata 4,000 a cikin kananan hukumomi 27 da ke Jihar Jigawa ne za su amfana daga wannan shiri na Gwamnatin Tarayya na bada tallafin kudi ga matan karkara.
Minista Sadiya Umar Farouk ce ta bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da shirin wanda aka yi a Dutse, babban birnin jihar.
Ta ce, “Ina ta lura da kokarin inganta jihar wanda mai girma Gwamna ke yi, kuma na tabbatar idan an ci gaba da wannan gagarumin aiki, to, tsare-tsare da shirye-shirye daban-daban da gwamnatin Shugaba Buhari ke yi za su yi tasirin da ake bukata a rayuwar al’ummar Jihar Jigawa.”
Ministar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a lamarin da su mara wa Gwamnatin Tarayya baya a kokarin da ta ke yi na magance matsalolin da su ka danganci cigaban kasar nan.
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, wanda ya yi magana ta bakin mai ba shi shawara na musamman kan karfafa tattalin arziki, Abba Muhammad Mujaddadi, ya yaba wa shirin na Gwamnatin Tarayya, sannan ya yi la’akari da cewa Jihar Jigawa ta amfana da sauran shirye-shiryen magance fatara na Gwamnatin Tarayya a baya, wato irin su GEEP, CCT, HGSFP, da sauran su.
Gwamnan ya yi kira ga wadanda su ka ci moriyar shirin da su yi amfani da kudin ta hanyar da ta dace domin taimakon kan su da iyalan su.