Sama da mata 12,000 da ke karkara a fadin kananan hukumomi 71 da ke Jihar Kano da Jihar Jigawa suka amfana da tallafin naira 20,000 ga kowacce, karkashin shirin tallafa wa matan karkara na gwamnatin tarayya. Mata guda 8,000 da ke fadin kananan hukumomi 44 a Jihar Kano suka amfana da wannan tallafi, yayin da mata 4,000 da ke fadin kananan hukumomi 27 da ke Jihar Jigawa suka amfana.
Ministar jinkai, Sadiya Umar Farouk ita ta bayyana hakan wajen kaddamar da shirin tallafin a Jihar Kano da Jigawa. Da yake magana a matsayin wakilin ministar a Kano, sakataren dun-dun-dun na ma’aikatan jinkai, Bashir Nura Alkali ya bayyana cewa, ministar ta ce an fara samar da wannan tun a shekarar 2020, domin cika burin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“An samar da wannan shirin ne domin tallafa wa mata talakawa da mabukata da ke cikin yankunan karkara da kuma burane a kasar nan.
“Tsabar kudade na naira 20,000 ake rarraba wa mata talakawa kimanin 125,000 da ke fadin kasar nan ciki har da babban birnin tarayya.”
Da yake gabatar da jawabi, gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yaba wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen gudanar da shirin tallafa wa talakawa da mabukata a cikin al’umma musamman ma mata da yara. Ya kuma nuna godiyarsa ga ma’aikatan jinkai da ta yi kokarin kawo aikin zuwa Jihara Kano. Ya ce, karkashin wannan shirin na raba tsabar tallafin kudade, an samu karan mata 35,000 suka amfana da shirin a kananan hukumomi guda 15 da yanda a baya akwai mata 35,000 da suka amfana, lallai wannan shiri abin abin a yaba ne. gwamnananm wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, , Dakta Alhaji Usman Alhaji ya bukaci a fadada shirin a sauran kananan hukumomi guda 29 domin a samu karin wadanda za su ci moriyar shirin.
Hakazalika, mata guda 4,000 da ke fadin kananan hukumomi guda 27 a cikin Jihar Jigawa suka amfana da shirin gwamnatin tarayya na tallafa wa mata da ke yankunan karkara.
Ministar jinkai, Sadiya Umar Farouk ita ta bayyana hakan a harin Dutse babban birnin Jigawa.
Ta ce, “mun kaddamar da wannan shirin ne bisa cika burin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take wajen tallafa wa rayuwan mutanen Jihar Jigawa.”
Ministar ya yi kira da sauran masu ruwa da tsaki da su bayar da goyan bayansu ga gwamnatin tarayya domin magance matsalolin da ke fuskantar kasar nan.
A nasa jawabin, gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar wanda mashawarcinsa ta fannin bunkasa tattalin arziki, Abba Muhammad Mujjadadi ya wakilce shi, yay aba wa gwamnatin tarayya da gabatar da wannan shiri a Jihar Jigawa. Gwamnan ya bukaci madanda suka ci moriyar shirin da su tabbatar da sun yi amfani da wannan tallafin ta hanyar da ta dace domin tallafa wa iyalansu.