Salisu Dawanau">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Matan Kasar Sin Na Kokari Matuka Wajen Gwagwarmayar Kawar Da Talauci

by Salisu Dawanau
December 20, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
6 min read
Matan Kasar Sin Na Kokari Matuka Wajen Gwagwarmayar Kawar Da Talauci
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A kwanan baya, na kalli shirin bidiyon “GUDUNMAWAR MATA A YAKI DA TALAUCI” da sashen Hausa na CMG ya tsara da kuma watsa a shafin FACEBOOK na CRI Hausa. Yanzu ina son gabatar da ra’ayina game da shirye-shiryen bidiyoyi da suka gabatar.

Ko shakka babu, kowace kasa tana da dabarun da ta kan bi wajen taimaka wa al’ummarta don ganin ta fid da su daga kangin talauci, da kuma kara habakar jari da ci gaba da kuma inganta tattalin arziki.
A karkashin kasar Sin, ko in ce akwai kasashen duniya da dama wadanda har kullum suke bibiyar kasar Sin don yin koyi da ita don tabbatar da kulawar al’umma kamar yadda ya kamata. Cikin irin wadannan kasashe da ke yin koyi da kasar Sin har da kasa ta Najeriya da kuma wasu kasashe masu tasowa a fadin duniya.
A yau dai, babu wanda bai san yanayin yadda mata suka shiga wannan harka ta taimakawa ’yan uwa ba wajen ceton kai da juna a bangarorin sake-sake da noma da kirkire-kirkire don ‘a gudu tare, a tsira tare’ cikin nasara.
A ci gaba da bayyana abubuwan koyi daga kasar Sin, sashen ku ya kawo mana wasu shirye-shirye masu nagarta da kara wayar da kai da fahimtarwa, da kuma ilmantarwa kan gudunmuwar da mata ke bayarwa a kasar Sin don kara taimakekeniya da kawar da zaman banza da kuma kawar da talauci ga ‘yan uwa mata da ke karkara.
Mun kalli hotunan bidiyo da kuka nuna a shafinku na facebook, har kuma kafin wannan lokaci, mun yada (share) su ga abokai don su kara fahimtar yadda yanayin rayuwa ke tafiya a kasar Sin a bangaren kawar da talauci wadda mata ke yi, da kuma yadda gwamnatocin jihohi da na larduna ke yi don basu kwarin gwiwa ta yadda kowa zai amfana.
Mun kalli hotunan bidiyo guda biyar, inda malama Fa’iza Mustapha da makwabcinta malam Murtala Zhang suka kai ziyarar gani da ido a wasu larduna, inda mata ke taka muhimmiyar rawa wajen daidaita zamantakewa da yaki da talauci. Kuma a zahirin gaskiya wadannan hotunan bidiyo sun kayatar ainun. Ba abinda zamu ce sai godiya da jinjina gare ku domin ku kara fahimtar da masu kallo da bibiyar shafinku na facebook.
Bugu da kari, zai yi kyau a ce ku ci gaba da kawo irin wadannan hotunan bidiyo, a watsa su sosai domin nuna wa duniya namijin kokarin da bangarori ke yi a kasar Sin don dakile talauci a tsakanin ‘yan kasa.

samndaads

ZIYARA A JIHAR NINGXIA
Ziyarar malam Murtala Zhang da malama Fa’iza Mustapha a wannan jiha game da nuna gudunmuwar mata kan shirye-shiryen kawar da talauci ya kayatar sosai, kuma shirin ya bayyana abubuwan koyi ga kowa, ba mata kawai ba har ma da maza. Kuma shiri ne wanda, a ra’ayina, zai dace ku kara fadada shi nan gaba don ya kunshi wasu larduna saboda ilmantarwa da ‘kara fito da kasar Sin a fili’ da ke shirin.
A zahirin gaskiya, kasar Sin tana samun karin ci gaba da bunkasa, cikin natsuwa, musamman a wannan karni da muke ciki. Kuma kai ziyarar ta su zuwa wannan jiha ya kawo mana labaru masu kyau game da ci gaban mata, a kungiyance da kuma daidaiku, a fannin kiwo da noma da yadda mata ke yin aiki tukuru don taimakon juna, da kuma kaucewa daga akubar talauci.
Matan wannan jiha suna yin ayyuka cikin hadin kai a kungiyance, kuma hirarraki da malaman biyu suka yi da mata ya kara bayyana kyawawan tunani da matan ke da shi na yaki da talauci. Ayyukansu gwanin ban sha’awa.
Kamar yadda muka kalla a hotunan bidiyon, na fahimci akwai kamannin al’ada tsakanin matan da na Najeriya a bangaren sutura (yadda matan kan rufe kawunansu da kallabi ko dan kwali).
Noma da kiwo da saka, wasu ayyuka ne da ke da tsohon tarihi, a nan Najeriya, haka ma a tsakanin al’ummomin wannan jiha. Kuma, cikin hikima da kwazo, mata suna bayar da gudunmuwa mai tarin yawa a wadannan bangarori a jihar.
A nan Najeriya, idan ka ziyarci jihohin Nasarawa da Kaduna da Filato, zaka ga mata suna bayar da gudunmuwa wajen noman kayayyakin marmari ko na lambu. A wannan jiha ma dai, matan suna iya kokarin su a wannan bangare don taimakon kai da samar da cimata, da kuma kawar da talauci.
A wasu yankuna na kasata, ba safai a kan samu mata a harkar noma ba, amma dai a bangarorin kasuwanci da sake-sake mata kan tabuka abin kirki domin ci gaba, wanda hakan ya sha bamban da yanayin matan wannan jiha ta Ningxia.
Ina iya cewa, ziyarar malaman biyu, haske ne sosai ga masu kallo, kuma ko a lokacin da na yada (share) wadannan bidiyo a shafin facebook, abokai na da dama sun yi tsokaci da sharhi kan sha’awar da suka nuna, da kuma yaba abubuwan da suka kalla don muhimmanci da kayatarwarsa.
Malam Bahaushe kan ce, ‘himma, bata ga rago’. Saboda haka, jarumta da juriya da jajircewa a wajen mutun kan haifar da cin nasara da bunkasa a galibin harkokinsa na yau da kullum. Ina iya cewa, hotunan bidiyon baki daya abin yin nazari ne, kuma abin kara kwarin gwiwa ga maza da mata.
Hakikanin gaskiya dai, akwai tarin ilimi na hakika a wadannan bidiyoyi, kuma kamar yadda na ambata a baya, hotunan tamkar kalubale ne ga ayyukanku inda ya kamata ku ci gaba da kirkirar wannan yanayi don kara tallata kasar Sin a bangarorin da suka dace, musamman a lokacin da aka samu wata rashin jituwa ko fahimta game da wasu akidoji ko manufofin kasar.
Kana idan ka kalli hotunan bidiyon, akwai tarin ilimi masu nasaba da al’adu da yanayin halayyar jama’a da zamantakewar al’umma a karkara. Babu shakka, shiri irin wannan zai taimaka matuka gaya wajen zaburar da mata da sanya musu sabbin tunani da tsari ta yadda za su nemi na kan su ba tare da jiran a basu ba.
A duk inda mace take, kamata ya yi ta yunkuro, ta koyi wasu sana’o’i da za su kara taimaka mata don ciyar da kai da taimakawa iyali, da kuma samun kyakkyawar ‘yanci daga yanayin da ta samu kan ta. Saboda haka, galibin wadannan hotunan bidiyo darussa ne kunshe a cikin su, darussa wadanda suke da amfani ga duk kan wanda ya kalla.

ZIYARA A LARDIN JILIN
Tun daga abubuwan da muka kalla daga sabon filin jirgin saman Beijing muka fara kallon bunkasar da kasar Sin ta yi a bangaren sufuri. Mai kallo zai ga yadda kasar ta gyara wurare don kara inganta ci gaban da take da shi a wannan bangare mai tarin albarka da kawo kudaden shiga masu yawan gaske.
Masu iya magana na cewa, ‘noma tushen arziki’. Wannan labari haka yake, domin da ka kalli irin gudunmuwar da mata ke bayarwa a wannan lardin, zaka gano cewar sun yi dabara da suka rungumi bangaren noma a daya daga cikin harkokin da suke bi domin kawo karshen talauci.
Masu gabatar da shirin sun kai ziyara Changchun na lardin Jilin cikin annashuwa da zummar nuna mana yadda harkoki da ayyukan da mata ke gudanarwa na taimkakon kai don kaucewa daga talauci. An ce lardin ya shahara a fannin noman shinkafa a baya.
A kauyen, mata suna kokari sosai wajen gudanar da ayyukan gona da noman masara don ci da sayarwa da kuma sarrafa bawon masara don wasu bukatu. Mun kalli yadda mata, manoma kan sarrafa bawon masara wajen kere-keren kayayyakin amfanin yau da kullum na gida da kawa, kamar su jakar hannu da jakar kafada na mata da yadda matan kan rina bawon masarar don yin amfani da su. Wannan basira yana da kyau.
Kana, a wannan wuri, masu kallo sun ga yadda kungiyoyin mata kan taimaka wa juna don dakile talauci cikin hadin gwiwa. Suna koya wa juna basirar da suke da ita wajen sake-sake da sana’o’in hannu cikin nasara da annashuwa da jin dadi. Shirin ya kayatar da ni sosai, kuma na tabbata duk wanda ya kalli shirin zai yi na’am da tsarin, kuma zai samu sabon tunani kan gudunmuwar da mata ke bayarwa kan shirin dakile talauci da zaman dirshan a tsakanin al’ummomi.
Kamar yadda kuka bayyana a shirin, gwamnatoci daban-daban su ma suna taimakawa don tabbatar da samun daidaito ko hanyoyin da al’ummomin su za su amfana, haka tsarin ya kamata. Kenan, zamu iya cewa kungiyoyin mata suna samun kwarin gwiwa da tallafi daga gwamnatoci domin kara yalwa da yin nasara a fanni da shirin dakile talauci a kasar Sin.
Gudanar da ayyuka kullum, kuma akai-akai kan haifar da sabbin fasahohi wajen magance duk abinda kan taso na nakasu ga ayyukan da aka iya. Kenan ya zama dole sauran kasashen duniya su ci gaba da yin koyi da manufar Sin ko dabarun da take bi cikin tsawon shekaru da lokaci a fannonin ciyar da ci gaba cikin nasara da samun kyawawan abubuwan more rayuwa tsakanin jama’ar kasar. Rayuwar al’umma zata inganta, kasa zata samu natsuwa, sannan za a samu nasara a duk kan bangarori na rayuwa a kasa.
Shirin noma na zamani da kiwo da inganta tsarin kiwon lafiya da sabunta tsarin kasuwanci (maras shinge) da kasar Sin ke tafiya a kai za su ci gaba da bata damar samun nasarori cikin ‘yan shekaru kadan masu zuwa.
Kamar yadda na ambata a baya, shirin nan da kuka faro zai yi kyau a inganta shi, zai yi kyau a bunkasa shi ta yadda zai bamu karin damar sanin gudunmuwar da mata ke bayarwa a fadin kasar Sin a sauran fannonin da ba ku ambata ba a shirin da suka gabata. Mu dai shirye muke, a kullum, don mu kara yada shirin domin sauran wadanda basu da dama su kalla tare da mu ta facebook, su kuma sabunta tunaninsu kan manufofin kasar Sin, da kuma kara fahimtar kasar a wasu bangarori na rayuwar yau da kullum.
Yayin da wadannan hotunan bidiyo suka kara fadada mana tunaninmu kan matan kasar Sin ganin kokarin da suke yi a koda yaushe don inganta rayuwarsu, da kuma yanayin yadda ake tafiyar da rayuwa da zamantakewa a karkara, ina fata wadanda suka kalli hotunan za su kudura a zukatansu cewar su ma za su kirkiri sabbin hanyoyin sauyi da gyara a harkokin yau da kullum na tsarin rayuwa.
Hakika wadannan hotunan bidiyo za su yi tasiri sosai ga duk wanda ya kalla kuma ya yi nazari a kai, kuma sako ya kai ga kowa cewar hukumomin kasar Sin suna iya kokari wajen kyautata zamantakewa da rayuwar al’ummar kasar da ke zaune a karkara, da basu damar samun na kan su ba tare da yin maula ba ko roko ba. (Salisu Dawanau)

SendShareTweetShare
Previous Post

UNESCO Ta Sanya Wasan Taijiquan Na Sin Cikin Fasahohin Da Aka Gada Daga Kaka Da Kakanni

Next Post

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Sallami Jami’anta Hudu Daga Aiki

RelatedPosts

Dabarun Gwamnatin Sin Ya Baiwa Duniya Kwarin Gwiwar Tinkarar Kalubaloli

Dabarun Gwamnatin Sin Ya Baiwa Duniya Kwarin Gwiwar Tinkarar Kalubaloli

by Salisu Dawanau
17 hours ago
0

“Abin da babba ya hanyo yaro ko ya hau kololuwar...

Shugaban Kasar Sin Ya Yiwa Taron Davos Jawabi Ta Kafar Bidiyo

Shugaban Kasar Sin Ya Yiwa Taron Davos Jawabi Ta Kafar Bidiyo

by Salisu Dawanau
17 hours ago
0

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci...

Ko Akwai Yiyuwar Kyautata Hulda Tsakanin Amurka Da Turai Bayan Sabon Shugaban Kasar Ya Fara Aiki?

Ko Akwai Yiyuwar Kyautata Hulda Tsakanin Amurka Da Turai Bayan Sabon Shugaban Kasar Ya Fara Aiki?

by Salisu Dawanau
17 hours ago
0

Wasu kafofin watsa labarai na kasashen Turai sun taba yin...

Next Post
Hukumar ‘Yan Sanda Ta Sallami Jami’anta Hudu Daga Aiki

Hukumar 'Yan Sanda Ta Sallami Jami'anta Hudu Daga Aiki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version