Maman Ada" />

Matan Kasar Sin, Sun Zama Jaruman Kawar Da Talauci

Matan Kasar Sin

Ina ganin tun bayan fitowata daga kasar Sin, gaskiya ban taba sha’awar sake komawa kasar Sin ba, sai bayan da na kalli bidiyon “GUDUNMAWAR MATA A YAKI DA TALAUCI” da sashen Hausa na CMG ya tsara da kuma watsa a shafin FACEBOOK na CRI Hausa game da ziyarar aiki na malam Murtala da malama Fa’iza a lardin Jilin. Hakika, ko shakka babu na yi ta zumudin ganin yadda wannan ziyara tasu ta kasance a wannan yanki mai dogaro da aikin noma, inda aka dukufa tare da ban hannun gwamnatin tsakiya, wajen kawo wata kyaukyawar manufa tare dukkan masu ruwa da tsaki da hukumomin da abin ya shafa, domin nuna karara yadda kasar Sin ta shiga gaban kasashe wajen yaki da talauci a dukkan sassan kasar na ciki da waje, kuma aikin da ya kawo babban tasiri da mazauna yankunan karkara da masu dan karamin karfi, inda kuma wannan tsinkaye ya tabbatar da yadda gudummawar mata take a yaki da talauci, wanda taken wannan rangadi na gani da ido, ko kuma ace gani ya kori na ma’aikatan sashen hausa na gidan rediyon kasar Sin cewa da CRI suka kai a wannan lardin Jilin na kasar Sin. Da farko abin wannan wannan gajeren fim ya kawo ma tunanina shine yadda sinawa suke da karamci da kuma karrama baki, musammun ma baki daga kasashen Afrika, wannan ya kuma nuna yadda dangantaka tsakanin bangarorin biyu take kara dorewa, sannan abu na biyu, shine yadda hukumomin kasar Sin suke dukafa wajen kara inganta da kyautata jin dadin zaman rayuwar mazauna karkara musammun ma yankunan dake fama da talauci, ta hanyar bullo da hanyoyin yaki da rishin aikin yi da fatara, wannan kuma daga dukkan rukunonin al’umma. Na uku, wannan rangandi yayi nuni da yadda hanyoyin sadarwa na zamani suke babban tasiri wajen bunkasa ayyukan hannu da bunkasa kasuwanci, hakan ya tabbatar da cewa tafiya nada makoma mai haske tsakanin sana’ar hannu da cinikayya ta hanyar internat, sannan abu hudu yadda kuma wannan ziyarar gani da ido ta nuna bilhak da gaskiya yadda mata suka tashi tsaye tsayin daka a yankunan karkara da wauraren dake fama da talauci, suke nuna cewa babu raggo sai maraye. Gaskiya mutanen lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin, sun cancanci yabo, musammun ma mata, bisa yadda suke nuna himma da kwazo wajen tafiyar da ayyukansu na hannu ko sana’o’i domin kudin shiga, da kuma hucewa kansu takaici. Bangaren da yayi matukar ba ni mamaki shine yadda matan wannan yanki suka lakanci aikin sarrafa bawan masara domin sarrafa su zuwa kayayyakin ado da kuma za’a saida. Babban zarafin da mazauna yankin Jilin suke da shine yadda suka jajirce ga aikin noma, domin abu na farko da yazo a cikin tunanin malama Fai’za shine yadda gonakin masara basu karewa, kenan wannan ya shaida cewa masara daga cikin cimaka mai kawo babban alfanu ga sinawa na wannan lardi, sannan kuma duk wasu abubuwa da ake samu daga karen masara ko sandar masara, duk ana iya sarrafa su, kenan garin Daling na daga cikin garuruwan kasar Sin da aka fi bada karfi ga noman masara.  Ina mamakin yadda ake iya sarrafa bawan masara wato har ma a kera wasu abubuwan bukatun yau da kullum, kamar wata jakar mata, wani alabai, wasu kayan ado, hullunan mata, wani faifai, ka wasu kwanduna, da wasu butunbumin kayayyakin daban daban. Wadanan kuma ake shigar dasu a saida da daraja sosai. A cikin wannan rangadi, kuma na lura, da yadda mace kamar maza cewa da madam Zhou Yanwen tare da sauran mata na kungiyarsu suka hada karfi da karfe wajen tafiyar da ayyukan kungiyarsu ta mata yadda ya kamata, wato wannan kungiya, ta kunshi matan da aka ba horo iri daban daban, musammun ma kan yadda zasi iya sarrafa bawan masara zuwa wasu kayayyakin da zasu samun shiga kasuwa da kuma zasu burge mutane wato ‘yan kasar da kuma bakin dake zuwa yawon bude ido a kasar Sin. Yadda mata, a kasar Sin suke hada kansu domin gudanar ayyukan kansu da kansu ya nuna kokarin hukumomin kasar Sin a karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wajen baiwa matan kasar damar samun ‘yancin gashin kansu wajen tafiyar da harkokinsu na kawo ta su gudummawa ga cigaban tattalin arziki, zamantakewar al’umma da kwanciyar hankali. Tabbas mata a kasar Sin suna taka mihimmiyar rawa wajen tallafawa magabatan kasar yakin kawar da talauci. Hakika nay aba yadda kuma madam Zhou Yanwen take shugabantar wannan kungiyar mata, da yadda suke bada hidima domin cigaban wannan kungiya tasu, ba na mamakin wannan mata domin nauyi ne ya rataya gare ta na kula da bada horo ga mambobin kungiyar ta yadda su ma matan zasu kawo gudummawarsu wajeen yaki da talauci. Ina ganin wannan kwarewa da matan lardin Jilin suke da bisa ga wannan salon a sarrafa bawan masara da kuma ganyen masara, nada dogon tarihi, domin a ganina, wannan fasaha tana tare da wayin kai tun na kakanni da kakanni, kenan anan ma wata dama ce ta nuna cewa rike al’adun gargajiya suna babban alfanu ga cigaba duk wani yanki ko wata kabila, a kasar Sin. Haka kuma wannan aikin gani da ido na ma’aikatan sashen hausa na rediyon kasar Sin, ya bani damar fahimtar wani muhimmin tashi tsaye domin neman na kai, sabanin abubuwan da muke cin karo dasu a kasashen mu na Afrika, musammun ma a shiyyar yammacin kasashen Afrika, inda ake ganin yawan mabarata a kan titunan manyan birane da kauyuka suna bara, maimakon neman aiki yi, wasu da karfinsu, wasun kuma suna fama da nakasar da ta shafi gangar jikinsu. Wannan al’amari na yawan barace barace na karya mutuncin mutane da kuma maida kasa baya. A cikin wannan bidiyo, na ga wata jaruma baiwar Allah duk da cewa tana fama da nakasa, bayan kuma maigidanta ya je ci rani, wannan bai hana ta ba, tafiyar da aikin hannu wanda a cikinsa da ta gwanance matuka. Madam Liu tana tana sarrafa kayayyaki daban daban da ganyen masara, kuma kai tsaye tare da abokan cinikayya dake nan kasar Sin da sauran kasashen duniya ta hanyar yanar gizo. Anan ina ganin babban cigaba ne mata a kasar Sin, suka samu, musammun ma matan da ke yankunan karkara, na yin amfani da wannan hanya ta zamani wajen tallata kayayyyakin da suke kirkirowa. Babban abin azo, a gani ne, dake tabbatar da matakan da hukumomin kasar Sin suka dauka kuma suke cigaba da dauka sun taimaka kuma suna cigaba da taimakawa mata sosai wajen neman na kai. Hakan kuma ya bayyana karara cewa mata a sassa daban daban na kasar Sin suna da wayin kai, kuma sun fita daga kangin jahilci, sabanin yadda muke fama da rashin ilimi da wayin kai na mata a kasashen mu na Afrika, musammun ma a wannan lokaci na cigaban kimiyya da fasaha. Kamar yadda malama Fa iza tace, bayan ta ga yadda wadannan mata suke amfani da cigaban kimiyya da fasaha, tare da hanyoyin sadarwa na zamani cewa da internet domin kara samun kudin shiga, wannan babban abin koyi ga shugabannin kasashe da kungiyoyin mata har ma da masu ruwa da tsaki ta fuskar cigaban mata dasu tashi tsaye nasu kawo gudummuwarsu ta yadda su ma matan Afrika zasu iya amfana da irin wadannan hanyoyi domin su ma su baje kwarewarsu ta hanyar kayayyakin da suke sarrafawa na hannu. Dole na jinjinawa, babban gidan rediyon kasar Sin, musammun ma, sashen hausa, bisa ga namijin kokarin da ma aikatan suke yi wajen kara cigaban da kasar Sin take samu koda yaushe: wato ta fuskar tattalin arziki, zamantakewar al umma, da zaman karko bisa manyan tsare tsare daga dukkan fannoni. Wannan shirin da aka bullo da shi, mai taken: Gudummawar mata a yaki da talauci a kasar Sin, musammun ma a yankunan karkara da kuma yankunan da ke fama da talauci, shiri ne dake tabbatar da babbar gudummuwar da matan kasar Sin suke kawowa kasarsu, wannan ya nuna yadda matan birane dana karkara suka hada karfi da karfe, wajen neman yancinsu ta fuskar tattalin arziki da cigaban kasa mai dorewa. Yadda kasar Sin take samun cigaba cikin sauri, idan aka kwatanta da sauran kasashen da suka cigaba kamar Amuraka, Canada ko Amurka da wasu kasashen tarayyar Tura, ya bayyana cewa al ummar sinawa da shugabannin kasar Sin a karkashin jagorancin shugaban kasar Sin kuma babban sakatare janar na jam iyyar kwaminis ta kasar Sin, mai martaba Xi Jinping suna aiki kafa da kafa domin moriyar kasar Sin guda tak a duniya. Babbar narasa ce, wannan jan aiki game da gudummuwar mata a yaki da talauci a kasar Sin, kuma dole ya zama abin koyi ga kasashen Afrika da ma sauran kasashen duniya, idan ha rana neman kawo karshen talauci daga wajen mutane. Kasar koda yaushe tana zama wani babban misali, wajen tsinkayen abubuwan da zazu taimakawa kawar da talauci a doron duniya: haka zai tabbata idan ha rana baiwa mata damar gudunar da ayyukan cigabansu kamar yadda kasar Sin take yi. Idan aka duba, wannan shiri na baiwa mata horo domin neman na kansu, a lardin Jilin kawai ya zarce fiye da dubu goma na matan da suka ci gajiyar wannan horo da kuma basu damar fita daga kangin talauci a duk fadin kasar Sin, haka kuma wata babbar daman a bunkasa kayayyakin hannu dana gargajiya na kasar Sin baki daya. A karshe abin da nike son in kara fadi game da wannan shirin mai taken gudummuwar mata a yaki da talauci a kasar Sin ya zama babbar manufa ta kawar da talauci daga wajen mata ganin cewa mata sun kasance rukuni mai rauni a tsawon lokaci, ana keben su, ba a damawa dasu a cikin harkokin yau da kullum, amma tun yau da yan shekarun baya bayan nan, mata sun fara shiga gaba a cikin harkokin siyasa, tattalin arziki da zamantakewa, wannan ya kai mata a yau sun zama wani babban rukuni mai rinjaye bisa ga yawansu a doron duniya, wannan babbar zarafi ga kasashen duniya, dalilin Kenan da kasar Sin ta kasance ta farko a duniya wajen neman kyautata jindadin rayuwar mata ta hanyar basu damammakin nuna kwarewarsu da kwazonsu da ma kishin kasarsu na zama babban gishikin dorewar cigaban kasarsu: matan kasar Sin, sun zama jaruman kawar da talauci.

 

Exit mobile version