Daga Bello Hamza,
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa, matan Nijeriya sun cancanci karin kulawa ta yadda za su bayar da gudummawarsu a dukkan fannonin rayuwar al’umma.
Gwmnan ya yi wannna tsokacin ne a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a wajen wasan kwallo na musamman na mata don bikin ranar mata na duniya da ake cigaba da gudanarwa.
Ya ce, mata na fuskantar manyan matsaloli masu yawa a fadin duniyan nan.
“A yau matanmu na fuskantar gasar kwallon kafa don bikin ranar nata ta duniya, wannan abin a yaba ne.
“Ya kamata a yaba da kokarin da mata ke yi a dukkan bangarorin rayuwa, ba za mu yarda da kin ba mata kulawar da ya kamata ba musamman in sun samu nasara a an duk abin da suka sa a gaba.
“Bai kamata a manta basu ba, ina mai kira da a bayar da kulawa na musamman ga mata, musamman a bangaren albashi da sauransu.
“Wannan kuma ba wai ya tsaya a bangaren kwallon kafa kawai ba ne, ya kamata a sa ido a kan dukkan bangarorin wasanni gaba daya,” inji shi.
Gwamnan ya kuma ce, jihar sa tana ba mata kulawa na musamman a dukkan bangarorin rayuwa.