Daga Khalid Idris Doya,
Matar jagoran ‘yan uwa Musulmi a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Al-Zakzaky wato, Malama Zeenatudden Ibraheem, ta kamu da cutar sarkewar numfashi ta Korona kamar yadda babban danta Mohammed Ibraheem ya shaida.
Zeenha da mijinta dai sun shafe tsawon lokaci a gidan yarin Kaduna sakamakon shari’arsu da ake yi tun bayan rashin jituwar da aka samu a tsakanin Sojoji da ‘yan Shi’ar a birnin Zariya watan Disamban 2015.
A wani sanarwar da babban danta Muhammad Ibrahim da ya fitar da yammacin nan, ya nuna cewar jikin mahaifiyar tasa ya tsananta bayan ga wasu cutuka da suke damunta an kuma tabbatar da cewa ta kamu da cutar Korona wanda ke hanzarin kisa.