Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Matar Almakura Ta Sallami ‘Yan Gidan Yari 70 A Nasarawa

by Tayo Adelaja
October 9, 2017
in RAHOTANNI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Zubairu T. M. Lawal Lafiya

Matar Gwamnan Jihar Nasarawa Hajiya Mairo Umar Tanko Almakura ta sallami mazuna gidan yari guda 70 a Jihar Nasarawa. Sallamar ta zo ne ta hanyar ƙungiyarr matar Gwamnan wadda ta daɗe tana fafutukar talla w al’ummar Jihar. Ƙungiyarr mai suna Tallafi ta gudanar da ayyuka dabam- dabam na jinƙai ga al’ummar Jihar Nasarawa maza da mata manya da yara.

Tallafin ya shiga lungu da saƙo masamman a yammacin jihar, inda yake taimaka wa marasa galihu. A wannan karon ƙungiyar mai suna tallafi ta kai ɗauki ga al’ummar da ke rayuwa cikin ƙunci a gidajen yari da ke faɗin Jihar Nasarawa.

Ƙungiyar ta yi afuwa ne ga matasa masu zaman waƙafi a gidajen kurkuku da ke jihar. Inda ya tuntuɓa laifukansu ya tarar ba wani lefi ne da yake da muguwar barazana ga rayuwar alumma ba. Sannan ta biya kuɗin diyar ko na ce tara da aka yi masu aka rubuta takardar sallama gare su. Ƙungiyar ta Hajiya Mairo Almakura ta gudanar da gagarumin biki na sallamar waɗanda ta biya kuɗin tarar a zauren taro na cibiyar Matasa mai suna Ibrahim Abacha da ke gari Lafiya.

Da take jawabi wajen taron Hajiya Mairo Umar Tanko Almakura wadda Tsohuwar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Nasarawa Hajiya Zainab T. Ahmad ta wakilta. Ta yi kira ga waɗanda suka samu wannan gata na sallamar su daga gidajen yari, ta hanyar biyan kuɗin fansa da su gode wa Allah da ya bai wa Hajiya Mairo damar shigowa ta ziyarce su. Sannan ta ji kokensu kuma ta share masu hawaye. Ta ƙara da cewa ya kamata su ɗauki darasi daga yanayin rayuwar da suka koyo daga gidan yari. Ta ce; rayuwar gidan waƙafi wata irin rayuwa ce ta dabam. Saboda haka su yi wa kansu nasiha su zama mutanen kirki cikin alumma. Ta ce duk da cewa wasu ba laifin sata ba ne ya kai su wannan gurin amma ya kamata su riƙa yin haƙuri da yanayin rayuwa. Ta ƙara da cewa; kamar yadda suka yi wa Hajiya Mairo alƙawarin cewa ba za su sake aikata miyagun laifukan da zai kawo su gidan nan ba to su cika alkawari kada su yi tubar muzuru.

Sannan ta yi kira ga sauran matasa da su riƙa kai hanakali nesa, kuma su riƙa yi wa kansu nasiha da kyawawan ɗabi’u. haka zalika ta yi kira ga masu hannu da shuni da su riƙa ziyartan irin waɗannan guraren suna ceto yaran da laifukansu bai kai ya kawo ba saboda ceto su tamkar ceton al’umma ne. Idan aka bar su suka haɗu da wasu miyagu sai su koyar da su wata muguwar ɗabi’ar da ta fi tasu sai su zo su addabi jama’a. Sannan ta miƙa kyautar Naira dubu biyar biyar ga mutanen saba’in ɗin da aka sallama, haka zalika ta miƙa buhun shinkafa goma da jarkar man gyaɗa biyar da kwalin magi biyar ga mazauna gidan Kurkukun.

Jama’a da dama sun yi kiraye- kiraye ga waɗanda aka sallamo da su daure wa zuciyarsu su riƙa aikata ayyukan alheri. An dai salami mutanen ne daga gidajen yari guda biyar wanda ya haɗa da gidan waƙafi na garin Lafiya da na Wamba da gidan Kurkukun Nasarawa da na garin Keffi guda biyu.

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Taraba Ta Yi Bajin Kolin

Next Post

Ranar Malamai: Buhari Ya Ba Wata Malama Ƙyautar Mota

RelatedPosts

ACF

Kungiyar ACF Da Badakalar Jagoranci A Yankin Arewa

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Zailani Bappa, Al’ummar Arewa da dama za su tabbatar...

NLC

Mafi Karancin Albashi: Wata Kungiya Ta Yi Tir Da Kalaman NLC Akan Dan Majalisa Datti Babawo

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Bello Hamza, Wata kungiya mai zaman kanta mai suna...

Abduljabbar

Abduljabbar Bai Kai Darajar A Yi Masa Gangami Ba –Sheikh Khalil

by Muhammad
2 days ago
0

Ya Ce, Dalilin Da Ya Sa Sarkin Musulmi Ya Hana...

Next Post

Ranar Malamai: Buhari Ya Ba Wata Malama Ƙyautar Mota

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version