Yusuf Shuaibu" />

Matar Aure Da Diyarta Sun Shiga Hannun ‘Yan Sanda Bisa Laifin Sayar Da Jariri

Jami'an

Rundunar ‘yan sandar Jihar Anambra, ta cafke wata matar aure tare da diyarta, bisa laifin satar karamar yarinya ‘yan shekara hudu. Matar mai suna Ngozi Ede da kuma diyarta mai suna Kosiso sun saida yarinyar ne a kan kudi naira 250,000. Lamarin dai ya auku ne a Awada cikin Obosi karamar hukumar Idemili da ke Jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Haruna Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga ‘yan jarida. mohammed ya bayyana cewa, an kwato yarinyar sannan an mika ta ga mahaifiyarta cikin koshin lafiya.
Ya ce, “Rundunar ‘yan sanda reshen Awada ne ta samu nasarar cafke Ngozi Ede ‘yan shekara 42, tare da diyarta Kosiso Ede mai shekaru 17, a gida mai lamba 4, a tashar Ukaegbu cikin Awada. “Wadanda ake zargin dai sun hada kai ne sannan suka sace yarinyar mai suna Mesoma Ikoko ‘yar shekara hudu daga wajen mahaifiyarta mai suna Nneka Ikoko da ke Mammy Market cikin barikin sojoji na Onitsha.
“Binciken da aka gudanar ne ta kai ga cafke Ifeoma Okeke mai shekaru 45, wanda ya amsa yarinyar daga hannun wadanda ake zargin, sannan ya mika ta ga Ifeoma Okonkwo da ke Eke Nkpor. “An kwato yarinyar da aka sace sannan an mika ta ga mahaifiyarta cikin koshin lafiya. Saboda haka, an kuma kwato naira 250,000, kudin da aka bai wa wadanda ake zargin na wannan mummunar kasuwancin.”
Kakakin ya kuma kara da cewa, ana gudanar da binciken lamarin, sannan idan aka kammala za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Exit mobile version