Khalid Idris Doya" />

Matar Firaministan Nijeriya Na Farko Ta Kwanta Dama

Hajiya Jummai Abubakar Tafawa Balewa wacce ita ce matar da ta rage na Fira Ministan Nijeriya na farko, Marigayi Abubakar Tafawa Balewa ta rigamu gidan gaskiya a Lahadin nan.
Majiya daga iyalai sun shaida wa wakilinmu a Bauchi da yammacin Lahadin nan cewar Hajiya Jummai ta rasu da safiyar yau Lahadi a wani asibiti da ke jihar Legas.
Majiyar ta kara da cewa, kwanan baya an kai marigayiyar asibiti a kasar Indiya domin nema mata kulawar likitoci kana an sallameta daga asibitin a makon jiya, inda ta dawo Nijeriya don ci gaba da jinya.
Majiya daga makusantan ya kuma kara da cewa matar jarumin Nijeriyan ta dawo Nijeriya inda ta tsaya a Legas domin hutawa daga bisani ta karaso jihar Bauchi domin ci gaba da kula da lafiyarta, “Abun bakin ciki, da safiyar yau Lahadi rashin lafiyar nata ya sake tashi inda har ta kai ga ta suma, daga bisani Allah ya dauki rayuwarta,” A cewar majaliyar.
Ana sa ran cewar za a dawo da ita jihar Bauchi a ranar Litinin domin jana’iza da kaita makwancinta na asali.
Cikakken labarin Rasuwar nata zai biyo baya
Exit mobile version