Matasa 1600 A Kano Sun Samu Aikin Yi Da Tallafin Naira Miliyan Biyu –  Gawuna  

Matasa

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna, wanda kuma shi ne kwamishan ma’aikatar gona ta Jihar Kano ne ya sanar da hakan ya yin nuna nasarorin da Gwamnatin Jihar Kano ta cimma a shekaru 2 kan karagar mulki a karo na biyu.

Dr. Gawuna wanda shugaban shirin noma domin kyautatuwar rayuwa wato APPEALS PROJECT Malam Hassan Ibrahim ya wakilta, ya shaidawa LEADERSHIP cewa shirin appeals ya samar da aikin yi ga matasa dubu daya da dari shida cikin shirin mata da matasa inda ko wane mutum ya sami sama da Naira Miliyon 2 a asusunsa don inganta rayuwar matasan Jihar Kano.

 

Ya ce,  yanzu haka kusan kaso 90% na matasan tuni sun samu kudaden a asusun bankunansu. A cewar Mataimaki na Musamman ga Mataimaki Gwamnan Jihar Kano,  a kan yada Labarai Bashir Idris Ungogo, tuni Gwamnatin Kano a fannin shirin noman damina, ta kammala shirye-shiryen da suka kamata don kyautata rayuwar Manoma ta fuskar samar da aabbin irin shuka mai habaka yawan amfanin gona da taki, da magungunan kwari.

 

A karshe an shawarci manoma da su hada kai tare da karbar shawarwarin malaman gona don samun nasarar da ake bukata.

Exit mobile version