Daga Lawal Umar Tilde Jos
Sannaniyar Cibiyar Horar da ma aikata na kasar nan Industrial Training Fund [ITF], ta fara horar da matasa dubu goma sha daya (11,000.) da suka fito daga kowane bangare na Tarayyar kasar nan.
Wannan bayainin na kunshe ne a cikin takardar da babban Jami’in hulda da jama’a, na Cibiyar Sleyol Fred Chagu, ya sanya wa hannu wanda aka rarraba wa kafofin watsa labarai a Jos a makon nan da ya gabata. Ya ce, wannan shirin wani bangare ne da gwamnati mai ci yanzu karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ya bullo da shi na samar wa dimbin matasan kasar nan maras aikin yi ayyukan yi.
Takardar ta kara bayyana cewa wannan shirin mataki ne na biyu, NISDP, na shekarar da ta gabata inda aka horar da matasa dubu goma daga jihohi 18, daga cikin jihohin kasar inda ake bukatar kowace jiha daga jihohi 36 da Abuja, su ba da matasa dari uku, inda za a horar da su a kan fannoni daban- daban wadanda aka sara za a gudanar a Cibiyoyi 3,700 a cikin kasar.