Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home Arewa Ta Yamma

Matasa Ku Ceto Nijeriya Daga Rugujewa –Gwamna Matawalle

by Muhammad
April 7, 2021
in Arewa Ta Yamma
3 min read
Matasa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya bukaci matasan Nijeriya da su farka wajen kare kasar daga rugujewa.

Gwamnan ya ce lokaci ya yi da ya dace matasa su tsunduma harkokin siyasa gadan-gadan tare da fadawa cikin masu cewa a yi cikin harkokin jam’iyyun siyasan da suke kasar nan domin su na da gurbi da rawar takawa.

Matawalle wanda ke wannan bayanin a jiya a garin Kaduna jim kadan bayan da ya amshi lambar yabo ta ‘Icon of Youth and Student Debelopment’ daga hannun kungiyar shugabannin matasa da na daliban Arewa (NYSF).

Gwamnan wanda ke samun wakilci daga dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe, Hon. Kabir Amadu Mai Palace a yayin taron.

Ya shaida cewa: “Ni ma matashi ne kamar ku, lokaci ya yi da ya dace ku shigo a dama da ku a fagen siyasa. Ba ku da wani dalilin kin yin hakan. Wannan kasar ta mu tana kusa da rugujewa hanya mafi dacewa na cetota daga hakan kuwa kawai shine ku matasa ku tashi tsaye wajen ceto ta.

“Akwai gayar muhimmancin matasa su kara kutsa kai cikin lamuran siyasa. Idan muka duba yawan adadin al’umman kasar nan za mu fahimta matasa ne ke da rinjaye. Don haka, lokaci ne da ya kamata a samu matasa na tururuwar shigowa cikin siyasa domin gudanar da shugabanci da jagoranci na kwarai domin kai kasar zuwa mataki na gaba.

“A siyasar ‘yan Nijeriya, da zarar ka kira matasa da su shiga siyasa, tambaya ta farko da matashi zai maka shine a ina zai samu kudin da zai tafiyar da harkokin siyasa da su?. Kawai mutum ya fara sanya wa ransa jin shiga da kuma son kasancewa a cikin siyasar zai kai ga nasara.

“A kowani lokaci ina fada, matsalar matasanmu a wasu lokutan daga garesu yake fitowa, matasanmu su ne ke sanyaya wa kansu da kansu guiwa. Idan matasanmu suka yi umumu suka fito a matsayin gungu guda, da yawan kuri’unmu na matasa za mu iya kafa shugaban da zai jagoranci kasar nan har zuwa matakin mukaman kasa zuwa na kansila duk matasa ka iya nasara.”

Gwamna Matawalle ya cigaba da cewa: “Idan matasanmu suka himmatu a fagen siyasa, za su iya kawo nasarar zuwa da jam’iyya wacce za ta saukaka musu da saida fom cikin sauki daidai da matakinsu na matasa, kuma su dumfari siyasa har zuwa ga samun nasara domin su na da tulin kuri’un da za su iya sauya komai.”

Ya daura da cewa, “Kamar yadda kuka sani ne, tun lokacin da na zama gwamnan jihar Zamfara a ranar 29 ga watan Mayun 2019 na maida hankali wajen kyautata ilimi da samar wa matasa ayyukan yi da na dogaro da kai domin kare rayuwar matasanmu a nan gaba da kuma aza-tubalin kyautata rayuwar shugabanninmu na gobe.

“Kuma, na bada fifiko wa bada tallafin karatu wa dalibanmu a kasashen waje irin su Sudan, Cyprus da India gami da sauransu da suke karantar ilimin likitanci, harhada maguna, Injiniyanci da ilimin zane-zane gami da saura wadanda daruruwan matasanmu suka amfana,” a fadin gwamnan.

Tun da farko a jawabinsa na lale, babban sakataren kungiyar matasa da daliban Arewa (Northern Youths and Students Forum’, Malam Aliyu Ahmad, ya shaida cewar sun baiwa gwamnan lambar yabon ne bisa cancanta da dacewa da kuma irin gudunmawar da ke yi wa matasa, mata da kuma al’umman jiharsa wanda hakan ya jawo cigaba sosai a jihar.

Ya ce, suna bada irin wannan lambar yabon ne domin karfafa wa shugabanni guiwa su kara himma wajen gudanar da kyakkyawa kuma nagartaccen shugabancin raya al’umma.

SendShareTweetShare
Previous Post

Shimfida Game Da Zamantakewa A Kasar Hausa

Next Post

Cikin Jerin Arziki Goma, Da Daya Kawai Amurka Ta Fi Nijeriya -Sheikh Khalil  

RelatedPosts

Albashi

Raguwar Kason Gwamnatin Tarayya Ya Hana Mu Biyan Albashi Mafi Karanci – Gwamnatin Kano

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa...

Kasuwan Katsina

Gobara: Ganduje Ya Bai Wa ‘Yan Kasuwan Katsina Taimakon Naira Miliyan 20

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga El-Zaharadeen Umar, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya...

Fawa

 Sana’ar Fawa Gado Na Yi Ba Taka Haye Ba -Sarkin Fawan Danmagaji

by Muhammad
2 weeks ago
0

Wakilinm da ke Zariya ISA ABDULLAHI GIDAN ‘BAKKO, ya samu...

Next Post
Amurka

Cikin Jerin Arziki Goma, Da Daya Kawai Amurka Ta Fi Nijeriya -Sheikh Khalil  

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version