Matasa Ku Gyara Halayenku Don Gobe, Cewar Ustaz Abu Bilal

gyara

Daga Ahmed Muh’d Danasabe

An yi kira ga matasa Musulmi da su gyara halayensu ganin cewa su ne manyan gobe wadanda zasu bada gudunmawarsu wajen ci gaban addinin musulunci da kuma al’umma,tare da sanin cewa watan wataran zasu koma ga mahaliccinsu.

Shahararren malamin addinin musuluncin nan da ke garin Lokoja, Ustaz Yahaya Abubakar, wanda a ka fi sani da Abu Bilal ne yayi kiran a yayin da ya ke gabatar da lakca a wajen bikin maulidin tunawa da ranan haihuwar Annabi Muhammadu ( SAW) wanda Alhaji Bashir Wanzami ya shirya a gidansa da ke unguwar Kura da ke birnin Lokoja a ranan asabar data gabata.

Ustaz Abu Bilal wanda shine babban limamin masallacin Isah Kutepa da ke Lokoja, ya ce ko zamanin manzon Allah( SAW) matasa ne su ka yi gwagwarmaya wajen gina addinin musulunci, a don haka, a cewarsa, gudunmawar da matasa su ka bayar wajen gina musulunci bashi misaltuwa.

A kan haka malamin addinin musuluncin ya kalubalanci matasa, musamman ma musulmi dasu guji aikata dukkan abubuwa da Allah( SWT) ya yi hani a aikata tare da gyara halayensu domin ganin sun zama jakadun musulunci na gari.

Ustaz Abu Bilal wanda ya nuna damuwarsa matuka ganin yadda matasa musamman na wannan zamani ke tu’ammali da miyagun kwayoyi da kuma shiga kungiyoyin asiri ya kuma ce Allah na matukar fushi da masu aikata ire iren wadannan abubuwa.

Malamin addinin musuluncin ya kuma bukaci musulmi da suyi koyi da kyawawan halayen fiyayyen hallita, Annabi Muhammadu ( SAW) wanda ya nuna kauna, hakuri da zumunci da kuma inganta zaman lafiya a lokacin rayuwarsa.

Daga bisani Ustaz Abu Bilal ya yi addu’ar samun zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmin duniya baki daya, inda a karshe ya yabawa Alhaji Bashir Wanzami, wanda shi ne ya shirya mauludin tare da yi masa addu’ar wanye wa da duniya lafiya.

Exit mobile version