Matasa Sun Banka Wa Wanda Ake Zargi Barawon Babur Ne Wuta

Kashe

Daga Khalid Idris Doya

 

Shalkwatar Rundunar ‘yan sandan jihar Benue a jiya Laraba ne ta ce, wasu fusatattun matasa suka cinna wuta ma wani matashi wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa har lahira a lokacin da ke kokarin satar wata Mashin a garin Makurdi.

Jami’in watsa labarai na shalkwatar Catherine Anene shine ya shaida hakan lokacin da ke ganawa da kamfanin dillancin labarai (NAN) ta wayar tarho a Makurdi.

Anene ya ce wanda aka kashe din ya kone kurmus ta yadda ba ma za a iya gane shi ba, yana mai cewa mai mallakin Mashin din shine ya samu karfin da ya yi kokuwar kare Mashin dinsa tare da jawo hankalin jama’an da suke kusa, lamarin da ya sanya matasa kai dauki wajen tare da banka ma barawon wuta ba tare da jiran-jira ba.

Kakakin ‘yan sandan wanda ya yi tir da wannan mataki na matasan, yana mai cewa ba za a iya gano asalin wanda aka kona din ba domin dukkanin kamaninsa an kone.

Wani ganau ya shaida cewa Barawon ya harbi mai Mashin din da bindiga amma ya gudu ba tare da alburushin ta sameshi ba.

Ganau din ya ce karar harbin ne ma babban abun da ya jawo hankalin matasa zuwa ga wajen, inda y ace mafi yawan matasan ‘yan Achaba da suka ji zabin lamari, sun kai ga cafke shi ne a daidai tsohon hanyar Otukpo da ke kusa da otel din Bobec inda suka cinna masa wuta a wajen.

Exit mobile version