Matasa Sun Datse Babbar Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

Daga Abubakar Abba , Kaduna

Gungun wasu matasa dake ƙauyen Sabon Gaya daura da Babban Titin Kaduna zuwa Abuja, sun fusata, inda suka datse babbar hanyar Abuja Zuwa Kaduna, babu shiga ba fita.

Matasan kamar yadda majiyarmu ta shaida mana sun ɗauki wannan matakin ne sakamakon kashe wani jagoran ‘yan sintiri  da wasu waɗanda ba a tantance ko su waye ba suka aikata, a lokacin da ya je gona. Sun tare babbar hanyar na tsawon awanni shida daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa 6:30 na yamma. Shi dai wannan ƙauyen na Sabon Gayan, tazaransa da Garin Kaduna Kilomita 23 ne.

Bugu da ƙari, hakan ya janyo tsaikon sufuri akan hanyar, inda kuma fasinjoji suka tsaya cirko-cirko.

Cikin abubuwan da Matasan suka koka akai har da matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙauyen nasu, sun kuma lashi takobin ba za su bar kan titin ba sai har gwamnati ta yi masu alƙawarin bai wa yankin kyakkyawan tsaro da kare lafiyarsu data dukiyoyin su.

A cewar matasan,”Ba wai muna son tada zaune tsaye bane, muna so ne gwamnati ta samar mana da wadataccen tsaro, ba wai kawai a riƙa zuwa ana yi mana daɗin baki ba lokacin da ake buƙatar ƙuri’un mu.”

A ƙarshe, matasan sun ce, “Har yanzu gwamnati ta gaza wajen kawo ƙarshen yin garkuwa da mutane da fashi da makami da yawan kai hari da kashe mutane da sauransu dake aukuwa a yankin mu.”

Exit mobile version