Khalid Idris Doya" />

Matasa Sun Jinjina Wa Gwamnan Bauchi Kan Aikin Masaukin Alhazai Na Zamani

Matasa

Wasu matasa a Jihar Bauchi sun yaba wa Gwamnan Sanata Bala Mohammed Abdulkadir, saboda gina katafaren Masaukin Alhazai da kuma ayyukan raya kasa da ya ke yi a jihar Bauchi.

Mai magana da yawu matasan Mu’azu Almustafa Galaje ne ya yi wannan yabo lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Sakatariyarsu da ke, ya ce “A gaskiya irin ayyukan raya kasa da Gwamna ya ke yi abin alfahari ne garemu, mussamman masaukin Alhazai irin na zamani da ake ginawa a kusa da filin Jirgin Sama na kasa da kasa na Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.”

Mu’azu, wanda shi ne shugaban kungiyar ‘Kaura Allah Maimaita Ma Na’ kuma mataimakin sakataren kare muradun gwamnatin jihar Bauchi, ya ce gwamna Bala ya himmatu wajen sabuntawa da inganta jihar Bauchi don habe suke mara masa baya don ya kai ga cimma nasarorin da ya sanya a gaba.

Ya ce, masaukkin bakin na dauke da dakunan kwana da bayan gida da masallaci wanda hakan zai sauwaka ire-iren wahalhalun da alhazai ke fiskanta lokacin tafiya aikin Hajji.

Da ya juya kan sauran ayyukan raya kasa Galaje ya ce ire-iren hanyoyi irin na zamani da Gwamnan ke ginawa a Jihar Bauchi, “Musamman  hanyoyi irin nazamani abu ne da zai bude garin ya bunkasa tattalin arzikin al’ummar ya kuma kawo ci gaba a garin wanda abu ne da gwamnatocin da suka gabata basu sami damar yi ba.”

Ya kuma gode wa gwamnan saboda yadda ya gyara makarantun firamare fire da 400 a dukkan lunguna da sako dake jihar Bauchi, wanda a baya wadanna makarantu suna cikin halin rashin tabbas.

Galaje ya kuma roki gwamnan da ya kara fito da ayyukan da za su rika taimakon talakawa musamman ma matasa, domin su sami yanda za su za su dogara da kansu, kuma su samu guraben da za su koma makaranta.

Ya kuma roki gwamnati da ta bude guraben da za a dauki matasa ayyuka domin su sami madafa a rayuwa.

 

Exit mobile version