Jama’a mazauna kauyen Sabon Garin Nasarawa da ke Karamar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina sun zama jajirtattu, kamar yadda jaridar Katsina Post ta wallafa. Jama’ar sun tattara duk wata jarumtarsu tare da yin gaba-gaba da wasu ‘yan bindigar daji wadanda suka kai musu hari a sa’o’in farko. Kamar yadda rahotanni daga Katsina Post suka bayyana, ‘yan bindigar masu tarin yawa a kan babura sun tsinkayi kauyen wurin karfe 12:30 na rana.
Sun yi awon gaba da dabbobinsu, kayan abinci da abubuwa masu muhimmanci na jama’ar kauyen. Amma kuma bayan da ‘yan bindigar suka sakankance cewa sun yi nasara, matasan sun yi jarumta inda suka zagaye gonaki tare da dazuzzukan da ke kusa.
Rahotanni sun bayyana cewa, matasan sun yi nasarar kashe daya daga cikin ‘yan bindigar tare da kwato dabbobinsu da suka sace. Amma kuma, a wannan karon, ‘yan bindigar sun kashe daya daga cikin mazauna kauyen tare da raunata wani, wanda a halin yanzu ya ke gadon asbiti inda a ke kula da shi.
A wani labari na daban, dakarun rundunar Operation Sahel Sanity sun kashe ‘yan bindiga biyu, sun damke 12 daga ciki tare da ceto wasu jama’a masu yawa da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Zamfara a makon da ya gabata. Wannan na kunshe ne a wata takardar da mukaddashin Daraktan yada labarai na hukumar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya fitar a ranar Litinin. Onyeuko ya ce, “A ranar 28 ga watan Augustan 2020, dakarun sojin Nijeriya da ke Maru sun kai wa wasu da ake zargin ‘yan bindiga samame yayin da suke kokarin shiga kauye Gobirawa. “Cike da kwarewar dakarun tare da taimakon ‘yan sa kai, sun hana ‘yan bindigar shiga kauyen.
“Yayin samamen, dakarun sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar inda suka kashe biyu daga ciki, amma wasu sun tsere da miyagun raunika. An ga jini a kasa wanda ya bayyana hanyar da suka bi.”