Daga Hussaini Baba, Gusau
Kwamandar Jami’an tsaro na farin kaya, watau ‘Ciɓil Defence’ na Jihar Zamfara Daɓid R. Abi ya bayyanawa manema labarai nasarar da suka samu na cafke waɗanda suka addabi Gusau da fyaɗen ‘yan Mata har mutum huɗu a gadar Baga. Shugaban yayi wannan bayanin ne a ofishinsa da da ke Gusau, hedikwatar jihar Zamfara.
Kwamanda Daɓid Abi ya bayyana cewa; “Matasa huɗu ne suka kama wata yarinya a gadar Baga a cikin kango, sai da kowanne cikinsu ya yi amfani da ita, duk da kururuwar neman ɗauki da ta riƙa yi, kuma suka yi mata barazanar cewa idan bata yi shiru ba, kanta za ta tona wa asiri, tunda kusa da anguwarsu ne.”
Waɗanda su ka yi lafin sun haɗa da; Safiyanu Ibrahim, ɗan asalin Jamhuriyar Nijar ne, sai kuma Abdulmalik Abdullahi da Bello Umar da Shehu Ibrahim dukka cikarsu ‘yan jihar Zamfara ne. Sai kuma Aminu Ɗansagau daga ƙaramar hukumar Bakura wanda ya sato Mashin daga Ɗangibga kuma dubunsa ta cika wajen sai da shi a Bakura.
Kuma ya yi kira ga iyaye idan suna da yara kangararru su miƙa masa rahoto don basu shawarar yadda za su tafiyar da lamarin yaran nasu.
Wanda ya jagoranci yi wa budurwar fyaɗe, Sufiyanu Ibrahim ya bayyana cewa da yardar ta su ka yi kuma har ta ce, idan ta samu matsala za su siyan mata magani. Don haka, wannan kuskure ne kuma ya riga ya faru suna neman afuwa.
A ƙarshe Kwamnadan ya bayyana cewa mutum biyu cikin waɗanda su ka yi fyaɗen suna da cutar ƙanjamau, a rahotan da suka samu daga asibiti. “Da zaran mun gama bincike, zamu miƙa su kotu.” Inji Kwamandan
Ita kuma budurwar ‘yar shekaru 17 tana amsar magani sai bayan wata uku za a yi mata gwaji inji likita.