Mahdi M Muhammad">

Matasa Za Su Iya Canja Nijeriya, Amma Dole Su Bi Tsarin Siyasa – Nda-Isaiah

Shugaban kamfanin LEADERSHIP Group Limited, Sam Nda-Isaiah, ya bayyana cewa, matasan Nijeriya na da duk abin da ake bukata don sauya kasar nan, amma dole ne su shiga harkokin siyasa. Ya kuma bukace su da su yi aiki tukuru wajen zaben sabbin shugabannin kasar nan a shekarar 2023.

Da yake magana a ranar Laraba, a matsayin shugaban liyafar shugaban kasa da cin abincin dare na wasu likitocin magunguna wadanda ba da jimawa ba suka samu matsayi mai girma a aikin gwamnati, Nda-Isaiah ya yi takaicin cewa duk da cewa masu zanga-zangar  #EndSARS suna da niyya ta gaske, sun kyale wasu ‘yan daba sun gurbata zanga-zangar.

Ya kara da cewa, ‘yan sanda suna cikin matukar bukatar canji, duk da cewa, ‘yan sanda kamar yadda suke a yau suna bukatar a wargaza su kuma a sauya su da wasu sabbin tawagar ‘yan sanda da za su iya amfanar kasar.

Shugaban yada labaran ya bayyana cewa, “Ni dai a yadda na damu, ‘yan sanda a yau suna bukatar a wargaza su, ban san abin da suke yi ba, amma ba za ku iya ko gyara su ba, suna bukatar canji gaba daya. Ba za su iya kare ku daga Boko Haram ba, ba kuma za su iya kare ku daga masu satar mutane ba, ba za su iya kare ku daga ‘yan bindiga ba, to me ya sa za ku rike su?”

“An fara zanga-zangar cikin lafiya da lumana, amma abin da muka gani bayan gwamnati ta amince da bukatar su ta soke SARS, ba wani abu da ke kusa da zaman lafiya. Dangane da shawarar wargaza F-SARS, Nda-Isaiah ya ce, wannan shi ne abu mafi gaggawa da gwamnatin Nijeriya ta taba yi.

Ya yaba wa kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na maido da zaman lafiya, yana mai cewa, babu yadda za a yi mutane su rinka ruguza kadarori, domin babu wata gwamnati da zata tsaya tana kallon hakan.

Nda-Isaiah wanda kuma yana cikin kungiyar likitocin magunguna ta Nijeriya (FPSN), ya kara karfafa likitocin da ke hada magunguna da su shiga siyasa domin samun mukamai da za su kawo sauyi.

Shima da yake jawabi, Shugaban PSN, Pharm Sam Ohuabunwa, ya jaddada bukatar yin watsi da rarrabuwar kawuna tsakanin kwararru a fannin kiwon lafiya, yana mai cewa, irin wannan rarrabuwar kan da ke yawan bayyana a shugabancin bangarori ba ta da wata fa’ida. Musamman ya nuna fushinsa ga yanayin da wasu mutane ke ganin likita ne kawai ya kamata ya shugabanci bangaren kiwon lafiya, yana mai bayyana cewa, irin wadannan maganganun sun sabawa adalci na dabi’a.

Dangane da zanga-zangar da ke gudana, Cif Ohuabunwa ya ce, abin kunya ne a ce wasu matasa sun mutu don kasar ta canza.

Ya ci gaba da cewa, “A bayyane yake, abubuwan da suka faru kwanan nan sun nuna cewa tafiya ya kankama don kafa sabuwar Nijeriya, duk da cewa ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari na kyale matasa su bayyana abin da ke ra’ayin su.

Duk wadanda suka karbi kyaututtuka a wurin kwararrun likitocin magunguna ne da mambobin al’umma.

Wadanda aka karrama sun hada da, Pharm (Mrs) Olusola Idowu, Babban Sakatare, Ma’aikatar kasafin Kudi da tsare-tsare ta tarayya, Pharm Farouk Ali Salim, DG, kungiyar ka’idoji ta Nijeriya (SON), Pharm (Dr) Kelly Nwagha, Ag DG kuma Shugaba na Asusun kula da Inshorar zamani na kasa (NSIS).

Sauran sun hada da Pharm (Dr) Zango Mohammed, manajan darakta na likitocin NNPC, Pharm (Mrs) Christiana Akpa, janar Manaja, sashen kula da lafiya, hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta Nijeriya NPA da Pharm (Farfesa) Isa Hussani Marte FPSN, shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Borno.

Exit mobile version