Connect with us

LABARAI

Matasa Za Su Iya Ceto Siyasar Nijriya, Inji Aminu Wali

Published

on

Yanzu lokaci ya yi da za a kyale matasan basar nan sun shigo domin gyara harkokin siyasar Nijeriya ta yadda suma zasu zama abin koyi ga na baya .
Wannan bayani ya fito ne daga bakin jigo a cikin jam’iyyar PDP a basar nan da jihar Kano, sannan kuma tsohon ministan harkokin basashen waje Ambasada Aminu Bashir Wali, a lokacin da daraktocin yabin neman zaben Muhammad Sadik Wali, a matsayin Gwamnan jihar Kano a zaben 2019 suka kai mashi gaisuwar baramar Sallah a gidansa dake Kano.
Aminu Bashir Wali ya ce, idan aka bai wa matasan damar shigowa harkokin siyasa, babu shakka a matsayin suna masu matsakaicin shekaru za a samu abin da ake bubata na ci gaban basa da al’ummarta a matsayin suna manya zasu nuna masu hanyoyin da suka kamata su bi.
Tsohon Ministan harkokin basashen wajen ya bara da cewa, masu bananan shekaru suna da basira sannan zasu fi kowa fahimtar zamani sune kuma daidai da zamani. Aminu Wali, ya nuna matubar farin ciki da dan takarar na shi ya fito neman gwamnan jihar Kano a tutar jam’iyyar PDP duk mutumin da yake son alhairi ga wani to dole kuma ya sowa kan shi, mutanan da suka fito da Sadik Wali sun ga dacewar shi neda kuma cancanta saboda haka ina ta ya shi murna da fatan alhairi da fatan Allah ya ba da nasara.
Idan Sadik Wali ya samu nasarar zama gwamnan jihar Kano ya san zai iya domin mun san tarbiyar da muka ba shi a cewar mahaifin na dantakarar harkar samu ba ta gaban shi sannan zan yi bakin kobarina wajen taimaka mashi wajen tafiyar da gwmanati domin samun saubin rayuwa ga al’ummar jihar Kano.
Aminu Bashir Wali ya nuna banbancin siyasar yanzu data shekarun baya ya ce, siyasar baya ana yin tane bisa abida amma yanzu siyasar yanzu ba bu abida sai kawai domin abin duniya da kuma samun matsayi a gwamanati, siyasar yanzu sai an tafi a hankali da lura domin abain ya canza, idan dantakara zai tafi yawon neman amincewar jama’a sai ya kashe mabudan kudi.
Da yake jawabi ga manema labarai, dantakaran gwmanan na Kano, Alhaji Muhammad Sadik Bashir Wali ya ce, ya fito neman wannan matsayi ne domin kawo ci gaba ga al’ummar jihar Kano.
Sadik Wali ya bara da cewa, a matsayinsa na dan jihar Kano ya san matsalolin dake addabar jihar, da zaran ya samu nasara zai mayar da hankali a kai, musammam farfado da masana’antun jihar da suka durbushe sakamakon rashin hasken wutar lantarki, da kuma jawo masu zuba jari daga basashen wajen ta yadda za a samu aikin yi ga matasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: