Matasan APC Sun Bukaci Sauya Mazaunin Kotun Zaben Gwamnan Bauchi Zuwa Abuja

Matasan jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi, sun bukaci a sauya matsugunin gudanar da shari’a kan zaben kujerar gwamnan jihar Bauchi na shekarar 2019 da ake ci gaba da fafatawa.

Matasan jam’iyyar ta cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da sakatare janar na kungiyar, Malam Nasiru Cigari ya sanya wa hannu, ya shaida cewar sauya matsugunin gudanar da shari’ar zai kawo kwanciyar hankali da kuma tabbatar da bayar da kariya wa masu gudanar da shari’ar hadi da Lauyoyin da suke kare mai kara da wadanda ake kara.

Wannan kiran na zuwa ne biyo bayan rashin jituwar da aka samu a tsakanin magoya bayan gwamnan jihar mai ci da kuma tsohon gwamnan jihar a lokacin da gwamnan jihar Sanata Bala ya je kotun domin fara kare kansa dangane shari’ar da ke ci gaba da gudana a ranar 2 ga watan Satumba 2019.

Idan za ku iya tunawa dai, gwamnan Bauchi, Sanata Bala Muhammad yana fuskantar shari’a ne biyo bayan maka shi a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar da tsohon gwamnan jihar M.A Abubakar ya yi yana zargin an tafka magudi a zaben da ya gudana na gwamnan jihar.

A zaman da kotun ta gudanar jami’an ‘yan sanda sun harba barkonon tsohowa domin tarwatsa matasan APC da na PDP wadanda suka tayar da hargizi a lokacin da shari’ar ke gudana.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da sakataren kungiyar matasan APC reshen jihar Bauchi Malam Nasiru Cigari ya fitar a jiya, sun yi tir da wannan lamarin gami da zargin jam’iyya mai ci a jihar ce ta janyo hargitsin.

Kungiyar ta ‘APC Youths Parliament’ sun nemi babban mai shari’a na Nijeriya Justice Muhammad Tanko da ya sauya matsugunin gudanar da shari’a kan zaben gwamnan Bauchi daga jihar ta Bauchi zuwa Abuja domin tabbatar da gudanar da shari’ar cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tashin hankali ba.

Cigari ya shaida cewar yin hakan zai kawo kariya ga Alkalan da suke gudanar da shari’ar gami da Lauyoyinsu na jam’iyyar APC.

“Lamarin wanda ya faru ya haifar da tashin hankali da fargaba a zukatan Lauyoyinmu gami da dumbin magoya bayan jam’iyyar APC a jihar,”

“A bisa haka wannan kungiyar take mai bukatar babban Jojin Nijeriya da ya tabbatar da daukar dukkanin matakai na canza wurin gudanar da shari’a kan kujerar gwamnan Bauchi zuwa Abuja domin tabbatar da kare rayuka da dukiya da gudanar da shari’ar cikin kwanciyar hankali,” A cewar sanarwar.

Sai dai a martakaninsa, jami’in watsa labarai na jam’iyyar PDP, Alhaji Yayanuwa Zainabari ya musanta zargin, yana mai shaida cewar jami’an tsaro ne ke da alhakin bayyana matsalar tsaro ko kalubalen da ke akwai muddin akwai hakan, don haka ne ya shaida cewar bukatar sauya muhallin gudanar da shari’ar bai da wata madogara.

A zaman dai da kotun ta yi na karshe, Shugaban tawagar Alkalan da ke shari’ar, Justice Salihu Shuaibu ya dake ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Oktoba, 2019 domin zuwa matakin karshe don yanke hukunci kan wannan shari’ar.

Exit mobile version