Matasan Nasarawa Sun Ayyana Goyon Baya Ga Takarar Bashir Wada

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Sama da magoya bayan jam’iyyar PDP dubu ɗaya ne suka janye goyon bayansu ga ita PDP ɗin a cikin garin Minna da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Chanchaga, hakan ya biyo bayan neman amincewar Barista Bashir Wada Usman ga tsayawa takarar kujerar majalisar dokokin jihar Neja.

Magoya bayan PDP ɗin sun ce tsayar da Barista Bashir takarar kujerar ɗan majalisa mai wakiltar wannan yankin zai kawo wa ƙaramar hukumar Chanchaga ci gaba duba da irin gudunmawar da yake bayarwa a ɓangaren shari’ar da yake tsayawa marasa ƙarfi idan ta taso, dan haka tunda sun ga yana goyon bayan maradun APC sun amince da miƙa goyon bayan ga ita jam’iyyar APC ɗin tare da neman Baristan da ya amince da ƙudurinsu na tsayawa takarar.

Bukin goyon bayan APC ɗin da canja sheƙa daga PDP ya gudana ne a unguwar daji cikin garin minna.

Da yake zantawa da wakilin mu, Barista Bashir Wada Usman, yace lallai akwai magoya bayan PDP da APC da suke neman amincewa ta dan tsayawa takara kuma ka ga yau su suka shirya wannan taron suka gayyace mu dan mu ga irin haɗin kan da suke da shi tare da neman buƙatar amincewa ta na yin takara, yanzu ba lokacin kamfen ba ne amma zamu zauna mu tattauna da manya da sauran al’umma masu ruwa da tsaki a wannan ƙaramar hukumarta mu, inda mun cimma matsaya za mu sanar da duniya kuma zamu shirya taro dan jama’a su shaida.

Bisa tsarin doka hukumar zaɓe ba ta buɗe shafin kamfen ba tukun na, idan ta fitar da tsare-tsaren zaɓe a matsayin mu na masana shari’a da dokoki zamu nazarci komai. Sai dai abinda na ke gayawa jama’a su sani, wannan aikin babba ne kuma aiki ne da sai an haɗa hannu an yi shi tare, aikin majalisa ba aikin bada kwangiloli ba ne, ba kuma aikin zartar da aikace-aikace ba amma duk da hakan akwai gudunmawar da ɗan majalisa zai iya baiwa al’ummarsa.

Babban abinda na ke janyo hankalin ‘yan siyasa shi ne bin doka da oda, sannan a tabbatar duk wanda ya kai munzalin jefa ƙuri’a ya mallaki katin zaɓe dan da shi ne kawai za ka iya nuna soyayyar ka ga wanda ka ke muradi. Dimokuraɗiyya fage ne na tabbatar da haɗuwar kawunan jama’a wajen gina ƙasa da samar da ci gaba mai alfanu ga tattalin arzikin ƙasa.

Da yake ƙarin haske, shugaban ƙungiyar tallata muradun APC ta jihar Neja, Kwamared Nuruddeen Iliyasu yace wannan na nuna cewar jama’a sun waye wajen zaɓo mutanen da ya kamata su riƙa wakiltarsu, jam’iyyar APC ta zo da muradun ingantattalin arzikin ƙasar nan ne da samar da kyakkyawan yanayi ga ‘yan ƙasa dan haka zaƙulo irin su Barista Bashir Wada Usman abin a yaba ne, sanin kowa ne aƙidunsa da muradunsa tamkar ya kwafa ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Jama’a na neman wakilci na adalci, kuma gwamnati ba za ta iya tafiya dai-dai ba muddin ba ta samu ‘yan majalisu nagartattu ba, idan Barista ya amince da wannan ƙoƙon barar na jama’a tabbas 2019 Chanchaga za ta samu wakilci na gari a majalisar dokokin jihar a zango na gaba.

Kwamared Nuruddeen ya yabawa maigirma gwamnan Neja akan irin ayyukan raya ƙasa da yake ta famar kafa a faɗin jihar, lallai a baya an yi ɓarna kuma an kashe dukiyar jama’a ba bisa ƙa’ida ba, a wannan zangon bayan zuwan Alhaji Abubakar Sani Bello a matsayin gwamnan jiha ya ta ka rawar ganin da kowani ɗan jiha mai kishi zai na’am da shi.

Taron dai ya gudana a yau lahadi a tsakiyar Nasarawa C a unguwar daji wanda ya samu halartar manyan ‘yan siyasar ƙaramar hukumar ta Chanchaga da kuma tsohon kwamishinan kimiyya da fasaha ta jiha kuma jigo a jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Katcha, Alhaji Muhammad Abubakar Katcha.

 

Exit mobile version