Abubakar Abba" />

Matasan Nijeriya 10,000 Sun Samu Horaswar Gwamnatin Kasar Jamus

Kimanin matasa 10, 000 ‘yan Nijeriya sun amfana da horaswar  ilimin zamani da gwamnayin kasar Jamus ta yi a cikin shekaru biyu.

Jami’in hukumar kasar ta GIZ ta kasa da kasa Mista Horst Bauemfeind ya sanar da hakan a hihar sa jaridar LEADERSHIP a satin da ya gabata lokacin rufe taron shirn da ya gudana a garin Abeokuta cikin jihar Ogun.

Bauemfeind ya ce, shirin wanda aka wanzar dashi a karkashin bayar da horaswar sanin makamar aiki na  (TEBET), yana daya daga cikin ci gaban da aka rattabawa hannu tsakanin  Nijeriya da Jamus a yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 1974.

Ya ci gaba da cewa, shirin ya horas da matasa ‘yan Nijeriya su 10, 000 kai tsaye a jihohin Ogun da Filato daga watan Yunin shekarar 2016 zuwa watan Mayun shekarar 2018.

A cewar Bauemfeind, shirin ya mayar da hankali ne a fannin aikin noma ta hanyar gwajin kasar noma da kasuwanci da kuma noman rani.

Ya bayyana cewar, matasa 4,782 a jihar Ogun da kuma matasa 5218 a jihar Filato aka horas a karkashin shirin, inda ya kara da cewar, kashi talatin da tara bisa dari, a jihohin biyu mata ne da suka amfana a karkashin shirin.

A cewar sa, “munyi amannar cewar, horaswar za’a ci gaba da ita idan mun janye daga baya domin mun riga mun  kafa ginshiki akan wadanda suka amfana akan harkar kasuwanci.

Shi ma a nashi jawabin, wani kwararre akan shirin na jihar Ogun Ibrahim Aliyu, ya koka ne akan kalubalen da tawagar sa suka fuskanta a bisa kokarin su na samun matasa da zasu shiga cikin shirin na horaswar.

Aliyu ya zayyan wasu daga cikin kalubalen da suka hada da, jan ra’ayin matasan akan bukatar su rungumi shirin na horaswar.

A karshe ya ce, nuna gamsuwar da wadanda suka amfana da shirin, ya nuna cewar an samu nasara akan shirin.

 

Exit mobile version