Connect with us

MATASAN ZAMANI

Matasan Nijeriya Mu Farka Matukar Muna Son Ganin Cigaban Kasa

Published

on

Daga Ibrahim M. Nasir

Masu iya magana sun ce “matasa manyan gobe, wasu kuwa suka ce “matasa kashin bayan al’umma”, sannan wasu sun ce “sanin matsalar matashi sai matashi dan’uwansa”, masana kuwa suna danganta cigaban al’umma da gyaruwar matasan al’umma din.

Idan kuwa za mu duba da idon basira tabbas kuwa haka maganan take Kamar yanda tsohon shugaban kasa na soji da farar hula Olusegun Obasanjo yake cewa “inganta rayuwar matasa zai taimaka sosai wajan habbaka cigaban kasa da al’umma ”, amma ma’anar sa ta canja idan muka yi duba ga matasan wanna al’umma ta Nijeriya, matasan wannan kasa munyi watsi da al’amura da gwamnati takeyi a lokaci daya kuma munyi sakaci wajan bada gudumawar da zai’iya kawo gyara a cikin gwamnati da al’umma din.

Ko meye ya janyo haka? Wannan kuwa tambaya ce ba akanmu matasa kadai ba tambayace ga mu matasan da ita gwamnati kanta.  Amsar tambayan nan baida nasaba da sakaci da gwamnatin baya dana yanzu sukayi da al’umma gabadaya bama matasa kadai ba, a lokaci daya kuma, al’ummar tana gani ta zura ido kawai amma ta kasa haduwa da fidda murya daya tilo wanda da shi za ta rika kalubalantar gwammati  idan ta yi kuskure domin samun gyara da cigaban Nijeriya.

Matasa da yawa a cikinmu mun fidda rai ga gwamnati wajan tallafawa rayuwanmu saboda muna ganin gwamnatin ta gaza taimakonmu ta fannoni da yawa shi ya sa duk wani mataki da gwamnati take  aiwatarwa ko ta aikata bama nuna damuwa da nuna alhini.

Muna ganin gyaran Nijeriya sai wani ikon Ubangiji ! Mun manta da cewa ba wanda zai iya gyara mana kasar nan idan bamu ba da kanmu ba. Kar mu manta, sai da al’umma fa gwamnati za ta yi duk wani kudurinta, a cikin al’umma din nan matasa ne galibi kaga kuwa da muna nuna damuwanmu a kan matsalolin da muke gani da idanun mu kuma muna kokarin nuna wa gwamnati kuskurenta, da wanka ya biya kudin sabulu.

Wanna kuwa haka yake, duk kasar da matasan ta suka yi sake suka shashantar da lamarin gwamnati da cigaban kasarsu to ba shakka kuwa ta dauko hanyar durkushewa da kafafunta.

Mu dau misali da matasan wasu kasashen ketare, matasan nan sun jajirce wajan ganin kasashensu sun samu cigaba na fannin abubuwan more rayuwa da suka hada da Ilmi, kiwon lafiya, kafa Masana’antu, samun ayyukanyi, dss. Amma mu a nan Nijeriya akasin haka ne, matasa ba mu damu da abin da gwamnati take yi ba ko da kuwa ya shafemu ko bai shafa ba, al’amuranmu kawai muke yi, sai idan kana hira a majalisa sannan ne zaka ji ai gwamnati ta yi kaza da kaza sannan ka ce kayya! Kuma ka cigaba da harkokin ka kamar bakomai ba ne ba.

Wannan halin ko inkula da matasa keyi da rashin bibiyar meye gwamnati takeyi don cigaban kasa ya yi nakasu sosai ga cigaban kasar nan! Babban abunda ke ci mana tuwo a kwarya shi ne soyayya da muke yi wa wasu masu rike da madafun iko yana rufe mana ido wajan ganin kuskuren da suke aikatawa ballantana mu nuna musu kuskurensu su gyara.

Toh amma tambayar anan ita ce, ta wace hanya matasa za mu bi wajen nunar wa ga gwamnati kuskuren ta din, har ya kai ga an yi nasarar samun gyaran? Domin kuwa gwamnatin kasar ta yi aron wani tsarin tafiyar da gwamnati wanda bai yi daidai da yanayin yan kasar ba.

Da farko dai tunda muna da ‘yanci na fadar ra’ayin mu a dimokuradiyyance ( freedom of speech),wannan dama ce a garemu wajen fitowa gidajen rediyo da yin rubuce rubuce wanda za su tilasta gwamnati izuwa ga canja akalar mulkin ga cigaban kasa da ‘yan kasa a siyasance (positibe criticism). Sa’annan mu kula da ka’idojin wannan ‘yancin fadar ra’ayin dan gudun batanci ga gwamnati ko tayar da zaune tsaye, domin yancin gwamnati ne ta hukunta duk wanda ya tsallake iyakar doka.

An samu cigaba yanzu sosai a duniya, dandalin soshiyal midiya da kullum muke mu’amala da shi yana da matukar tasiri wajan yada labarai cikin kankanin lokaci sannan da soshiyal midiyan nan za mu iya kokarin nuna gyara, wajan fadakar da ‘yan’uwanmu matasa Akan lamarin gwamnati da fadar ra’ayinmu game da wani abu da gwamnati ta aikata amma mu sani muna bin ka’idoji dan guje wa muzgunawa daga hukumomi.

Kamar yadda na fada a baya cewa soshiyal midiya wata aba ce da ya kamata mu rika fitowa muna fada wa gwamnati kuskurenta amma mun yi shiru, to sai yaushe? Dan Adam ba ya sanin kuskurensa sai an fada masa, to me muke jira? Mun gani ai yadda karfin dandalin sada zumunta (social media) ya haifar da gyare-gyare a wasu kasashen domin samun cigaba.

Idan gwamnatin nan ta kawo cigaba mu ne muka samu cigaba. Matasa ne wadanda za su fi amfana a kan kowa. Muna fitowa  a duk wata halastacciyar hanya ta dimokuradiyya, kana daga dandalin sada zumunta (social media) mu rika yin rubuce rubuce a jaridun kasar nan da fitowa a gidajen rediyo, zanga zangar lumana, dss. Nuna wa gwamnati kuskurenta da kokarinta, shi ne hanyar da zai kai mu cigaba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: