Daga Rabiu Ali Indabawa,
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Adamawa ta cafke wani matashi dan shekara 23, Yusuf Jibrilla da laifin dabawa wasu matasa biyu wuka, inda ya kashe daya daga cikinsu. INNIGERIA ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a yayin daurin aure a Mayo-Nguli, Karamar Hukumar Maiha ta jihar.
An tattaro cewa wadanda lamarin ya rutsa da su, Sadik Hammadandi, mai shekaru 22, da Adamu Suleiman, mai shekaru 25, suna zaune a wajen taron bikin ne lokacin da wanda ake zargin, wanda aka ce dan kwaya ne, ya sha tabarsa. Su biyun sun nemi ya tafi ne saboda ba za su iya jure hayakin ba.
Wanda ake zargin sai ya fusata, ya fito da wuka ya daba musu.
An garzaya da wadanda aka kashe asibitin Maiha inda aka tabbatar da cewa Hammadandi ya mutu, yayin da shi kuma Suleiman ya tsira amma za a yi masa aiki.