Shekaru da dama da suka gabata, wani saurayi dan kasar Masar ya yi watsi da digirinsa na ilmin kimiya na kayan tarihi domin farautar kunamu a hamadar kasar da kuma gabarta, yana cire dafinsu, don amfani saboda yin magani.
Yana dan shekara 25, Mohamed Hamdy Boshta a yanzu shi ne mai Kamfanin ‘Cairo Benom Campany’, masu aikin kunamu da macizai fiye da dubu 80 a gonaki daban-daban a fadin kasar Masar, kuma an ajiye babbobin ne kawai don dafin su wanda ake amfani da shi a wajen yin magunguna.
Ya na amfani da hasken UB mai launuka wajen tatso dafi daga jikin kunamun, wanda giram daya na dafin zai iya samar da tsakanin allurai 20,000 zuwa 50,000 na riga-kafin dafi.
Giram tdaya na dafin kunama zai iya kaiwa dala miliyan 10, kuma mohamed ya fitar da shi zuwa Turai da Amurka inda ake amfani da shi don yin riga-kafin sauran magunguna, gami da yanayi irin su hawan jini.