Yusuf Shuaibu" />

Matashi Ya Mutu A Rijiya Saboda Wayar 3,000

Rijiyar da abin ya faru

Wani matashi mai suna Cisse dan shekara 26 da haihuwa, ya rasa rainsa a cikin rijiya lokacin da ya shi ga dauko wayarsa, a gida mai lamba 7 da ke kan titin Olanrewaju kusa da mahadar hanya ta Mohan cikin karamar hukumar Mushin ta Jihar Legas. An bayyana cewa, kudin wayar bai wuce naira 3,000 ba.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, Cisse ya shiga cikin rijiyar ne lokacin da wayarsa ta fada, lokacin da yake kokarin ciro wayar, sai ya yi tsalla a cikin rijiyar wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa har lahira.

Wani wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa mai suna Yinka ya bayyana cewa, domin yukurin ceto mamacin, ya sanar wa hukumar kashe gobara ta Jihar Legas, inda nan take suka isa wajen da lamarin ya afku. Jami’an hukumar kashe gobara sun tsamo gawar Cisse mace.

Mazauna yankin sun bayyana cewa, yadda Cisse ya mutu a cikin rijiyar lokacin da yake kokarin dauko wayarsa. Sun nuna lahinunsu inda suka daura wa Cisse laifin a kan mutuwarsa. Sun dai yi ikirarin cewa, a kwai hanyoyi da yawa da zai iya bi wajan ciro wayarsa a cikin rijiyar.

Wata mata mai suna Nancy Oparaocha, ta daura wa Cisse laifi wajen daukar wannan kasada ta shiga rijiya. Ta bayyana cewa, “wannan abun takaici ne a kan abin da ya faru, sai dai bai kamata mamacin ya dauki kasadar shi rijiya ba wajen ciro wayarsa wacce ba ta wuce naira 3,000 ba.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mukaddashin shugaban hukumar kashe gobata ta Jihar Legas, Margaret Adeseye, ta bayyana cewa, an samu nasarar ciro gawar Cisse daga cikin rijiyar, inda aka mika ta ga ‘yan sandar yankin Olosan.

Exit mobile version