Khalid Idris Doya" />

Matashi Ya Raba Kyautar Babura Da Kudi Albarkacin Kauran Bauchi

Wani Matashi mai suna Alhaji Muttaka Muhammad Duguri, ya rabar da kyautar Mashina da kudade wa matasa da matan da suka yi kokari wurin kawo gwamnatin Sanata Bala Muhammad a jihar.

Matashin wanda kuma makusanci ne na kut wa gwamnan jihar ta Bauchi, ya yi rabon ne a jiya, inda Matasa da kungiyoyin mata daban-daban suka amfana da tallafin nasa.

Da ya ke jawabi a wajen rabiyar, Alhaji Muttaka, ya ce ya dauki nauyin hakan ne lura da irin gudunmawar da Mata da matasan suka bayar wurin samun nasarar Bala Muhammad a babban zaben 2019 da ya gudana, yana mai fadin cewar a shirye suke su ci gaba da tallafa wa marasa karfi a cikin al’umma domin rage wa gwamnatin sabgogi.

“Duk da mu ba mu rike da wani mukami a gwamnatin nan, za mu ci gaba da yin irin wannan taimakon, matasan da basu samu cin gajiyar a yanzu ba, su tsumayemu za mu sake yin rabon nan gaba kadan, za mu ci gaba da yi har zuwa karshen gwamnatin nan.”

Daga bisani Muttaka sai ya gargadi matasan da su rage dogaro da komai sai an yi musu, yana mai cewa gwamnatin Bala a shirye take ta share wa matasa hawayensu matukar suka tashi tsaye da yin ababen da zasu taimaki rayukansu kai tsaye.

Daya daga cikin masu jawabi a wurin taron, shugaban matasan gidan Sanata Bala Muhammad, wato Bala Saleh Chiroma (Youth Leader), ya shaida cewar mata da Matasa sun taka gagarumar rawa wajen samun nasarar Gwamna mai ci, sai ya tabbatar musu da cewar Gwamnan ya fitar da tsare-tsare masu kyawu da za su taba rayuwar matasan kai tsaye.

Bala Youth Leader, sai ya misalta rabon da Muttakan yayi a matsayin ci gaba mai ma’ana, yana mai jawo hankalin ire-irensa da su ci gaba da yin hakan, “Gwamna yana son duk wadanda suke jikinsa su zama masu alkairi, don haka muma za mu yi koyi da irin wannan aiyukan alkairin,” A cewar Bala Saleh.

Ya ce, an shigar da tsarin kyautata wa matasa a cikin kasafin 2020 ta fuskoki daban-daban wadanda yake cewa za a fara ganin tasirinsu nan bada jimawa ba, sai ya nemi matasan da su ci gaba da mara wa gwamnatin Sanata Bala baya domin ta kai ga cimma nasarori da manufofin da ta sanya a gaba na sabunta jihar.

Wakilinmu ya nakalto cewar Mashina da suka hada da Roba-Roba da kuma ta Kabu-Kabu guda goma ne matashin ya rabar, inda kuma ya zabo wasu kungiyoyin maza da mata daban-daban ya basu tallafin kudade daga dubu 50,000 wasu kuma suka samu tallafin 100,000 daga hannun matashin.

A wani labarin makamancin wannan, wani dan jam’iyyar PDP a jihar ta Bauchi, Alhaji Sani Shehu wanda aka fi sani da Sanin Malam, shi ma yayi makamancin irin wannan rabon inda ya rabar wa matasa da mata kayyakin sana’a domin dogaru da kawukansu da suka hada da kwamfutoci, kekunan dinki da kuma injunan wankin kai ga mata.

Sanin Malam ya yi rabon ne a unguwar Doya ga mata da matasan da suka samu cin gajiyarsa.  Da yake jawabin dalilinsa na yin hakan, ya ce ya rabar da kayyakin ne domin ya karfafi yunkurin gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad na rage matsalar rashin aiyukan yi da matasa ke fama da shi a cikin jihar.

Shi kuma da ya ke jinjina wa Sanin, babban mai baiwa gwamnan Bauchi shawara ta fuskacin tsaro, Mr Markus Koko Yake ya kalubalanci wadanda suka samu cin gajiyar ne da su himmatu wurin yin sana’ar da aka tsammata daga garesu domin su ma su zama wasu a cikin al’ummu.

Sai ya yi amfani da damar wajen jawo hankalin matasa da su ke tsame kansu daga fadawa ababen da ka iya janyo tarnaki wa hidimar tsaro a kowani lokaci.

Shugaban unguwar Doya a bangaren koyar da sana’ar hannu, Malam Sunusi Yusuf Abdullahi ya nuna godiyarsu a bisa wannan tallafin, ya sha alwashin sanya ido kan wadanda suka ci gajiyar don tabbatar da sun yi amfani da ababen da aka ba su ta hanyoyin da suka dace domin cimma manufar yin hakan.

Exit mobile version