Matashi Ya Rataye Kansa A Gusau

Daga Hussaini Baba, Gusau

Abin al’ajabi da tausayi da ban mamaki bai ƙare wa a ƙasar nan. Wani Matashi wanda ba a san daga inda yake ba ya rataye kansa, a jikin Bishiya a Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara.
Mutumin da ba a iya gane daga ina yake ba kuma ko wanene, ya rataye kansa ne a Sabon Titin ’Yan Loto da ke kusa da masaƙa bayan Gidan Man A.A. Rano da ke Gusau.

Wannan abin alajabi da takaici ya sanya alumar garin Gusau cikin firgici da damowa rashin gane shi ne mutumin da kuma Ina yake da inda yafito da kuma mai ya jawomasa ya rataye kansa da kan sa ko kuma wasu suka rataye shi, wannan ne babu masani sai Allah.

Rundunar ’Yan sanda ta tabbatar da faruwar wannan abin ban takaici kuma ta ce ta nan tana zurfafa bincike domin gano musabbabin faruwar wannan abu. a ta bakin jami’in Hulɗa da Rundunar sa.

Exit mobile version