Umar A Hunkuyi" />

Matashiya Ta Damfari Wata Mace Naira 700,000 Kan Za Ta Kera Mata Dala Miliyan Daya

A ranar Litinin ce, Wata mata mai suna Titilayo Shittu, ta bayyana a gaban kotun majistare da ke Ebute Meta, ta jihar Legas, a bisa zargin da ake yi mata na damfarar wata mata tsabar kudi har naira 700,000, bisa yi mata karyar za ta buga mata takardun kudi na dalar Amurka, har dala milyan Daya.

Ana dai tuhumar matar ce a bisa aikata laifin hada baki, da kuma sata ta hanyar yin karya da kuma cin amana.

Sai dai, matar ta musanta aikata laifin da ake tuhumar nata da aikatawa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sajen Ola Adelowo, ya shaidawa kotun cewa, wacce ake karan ta amshi wadannan kudaden ne daga hannun wacce ke karan, Uwargida Bibian Uzor, bayan ta yi mata asiri.

Adelowo ya ce, wacce ake karan ta aikata laifin ne a watannin Afrilu da na Mayu na wannan shekarar a kan titin Jebba, Ebute Meta.

“Ta yi amfani ne da asiri wajen gargadin wacce ke karan nata, da cewa kar ta kuskura ta shaida wa wani abin da ke gudana a tsakanin su, in kuwa ta yi hakan, za ta mutu,” in ji mai gabatar da karan.

Mai gabatar da karan ta ce, wacce ake karan ta shaidawa wacce ke karan nata ne cewa, tana da bukatar kudin ne domin ta buga mata takardun kudi na dala har na dala milyan daya. Abin da kuwa ta tabbatar da cewa karya ne take yi mata.

Wannan laifin da ake zargin ta aikata ya sabawa sassa na, 168, 287, 314 da 411 na dokar aikata laifuka ta jihar Legos, 2015.

Mai shari’a a kotun, Uwargida Monisola Ayinde, ta bayar da belin wacce ake tuhumar a kan kudi naira 200,000 da masu tsaya mata biyu su ma a kan wannan kudin.

Ayinde ta ce, masu tsaya matan tilas ne su kasance suna da tsayayyen aikin yi.

Sai ta dage sauraron karan zuwa ranar 9 ga watan Yuli.

Exit mobile version