Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta bayyana cewa, matatan mai na kamfanin Dangote wanda a halin yanzu ake ginawa za su iya tace danyen mai ganga 650,000, inda hakan zai taimaka wa Nijeriya har ma da sauran kasashen Afirka.
Hadakar shuwagabannin kungiyar ’yan kasuwa da kungiyar man fetur da masu makamashi sun hadu suka samar da kungiya guda daya mai suna ‘IndustriALL Global Union’ sun bayyana cewa, matatan mai na Aliko Dangote zai yi matukar taimakawa. Shugabannin sun bukaci gwamnatin tarayya da bayar da duk wani goyan baya da yake bukata wajen kammala wannan aiki. Wanda a yanzu haka ana ci gaba da gudanar da aikin matatan ba dare babu rana.
Ana saran za a kammala wannan katafarin matatan mai a farkon shekarar 2021.
Shugaban hadakar kugiyar, Kwamared Babatunde Olatunji ya bayyana cewa, wannan matatan mai na kamfanin Dangote ya kasance jari ne ga Nijeriya ga dukkanin kasashen Afirka gaba daya. Ya kara da cewa, shuwagabannin sun hada kai da manema labarai wajen tallafa wa aikin matatan man na kamfanin Dangote da ke Jihar Legas. Ya ce, lokacin da shugabannin suka ziyarci matatan mai sun ga ci gaba da idanuwansu wanda zai dace da muradun dukkan wata kungiya da ke duniya. Haka kuma a cikin muradun kungiyan dai shi ne kare hakkin ma’aikata da gina karfin ikon kungiyar da yaki a kan kare kudaden ma’aikata.
“Bisa tsarin da ake kokarin gudanarwa na bunkasa tattalin arzikin Nijeriya, ya kamata a bullo da shirin da zai taimaka wajen bayar ta tallafin daki domin bunkasa bangaren noma don samun abinci da amfanin ganan da masana’antu ke sarrafawa,” in ji Olatunji.
Ya kara da cewa, kungiyarsa tana yaba wa Dangote bisa zuba jari irin wannan aiki a cikin kasa ta yadda mutane za su sami ayyukan yi tare da rage zaman kashe wando ga matasa. Ya bukaci masu hali a Nijeriya su yi koyi da Aliko Dangate wajen zuba jari a cikin kasar nan, wanda zai amfana kasar da kuma ‘yan kasan gaba daya.
A nasa jawabin, Issa Aremu a matsayinsa na shugaban ma’aikatan sarrafa auduga, ya bayyana cewa cikin sauki za a dunga zirga-zirga da man a tsakanin ‘yan Afirka da gudanar daa harkokin kasuwanci da samar da wadataccen mai a cikin gida Nijeriya. Ya kara da cewa, ya kamata shuwagabannin kowani yankin na Arewa da na yankin Gabashi da na yankin Yammaci da su yi amfani da kudaden da suke da shi wajen bunkasa harkokin noma da yadda Nijeriya za ta rage dogaro da mai a matsayin hanyar samun kudaden shiga. Ya ce, lallai wannan taimako ne ga kasa, sannan taimako ne da mutane wanda zai sa su sami ayyukan yi da rage wahalhalun karancin tace mai da ake samu a cikin kasar nan.