Kamfanin mai na Dangote ya sanar da rage farashin man fetur (PMS) a duk faɗin Nijeriya, wanda zai fara aiki a yau.
Bisa ga wani faifan bidiyo da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), sabbin farashin sun bambanta bisa yankuna:
– Legas: ₦875 a kowace lita
– Kudu maso Yamma: ₦885
– Arewa maso Gabas: ₦905
– Arewa maso Yamma da Tsakiya: ₦895
– Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu: ₦905
Kamfanin ya bayyana cewa sabbin farashin za su yi aiki a dukkan gidajen mai na abokan hulɗar su kamar MRS, Ardova Plc (AP), Heyden, Optima Energy, Techno Oil, da Hyde.
Don tabbatar da bin sabbin farashin, Dangote ya sanya lambobin waya biyu (+234 707 470 2099 da +234 707 470 2100) domin ba da rahoto kan duk wani gidan mai da bai bi sabon farashin ba.