Injiniya Adewale Ladenegan shine sabon Manaja Daraktan kamfanin matatar man fetur wato KRPC, a jiya Litinin ya kama aiki a matsayin sabon shugaban kamfanin.
A yayin tattaunawarsa da wakilinmu Abubakar Abba ya bayyana shirye-shiryen da manufofinsa a kamfanin kamar haka:
Tambaya: Muna yi maka barka da zuwa kuma zamu so mu san wanne kudiri kake da shi akan kamfanin KRPC?
Adewale: Kudurin da nake da shin a farko shi ne samarwa da KRPC kudin shiga don habaka matsayin da Kamfanin yake
a yanzu, hakan zai kara samarwa da kasar kudin shiga yayin da kuma dimbin ‘yan Nijeriya za su amfana da man da ake fitar wa a kamfanin.
Adewale : Dukkan su mun dade muna aiki tare dasu kuma KRPC data Warri danjuma ne da dan Jummai domin kusan irin aiki daya ne muke gudanar wa, Dukkan matatun biyu suna kokarin su kafin wasu ‘yan matsaloli su kunno kai kuma insha Allahu za’a magance hakan don ganin kamfanin yaci gaba da aiki gadan-gadan kamar yadda matatar mai ta Warri ke aiki.
Tambaya: Shugaba kazo dai-dai lokacin da ake fuskantar kalubale na ma’aikata, musamman in aka yi la’akari da wasu lamurra tsakanin mahukuntan kamfanin da na ‘yan kungiya, wanne shiri ka ke da shi don warware hakan?
Adewale: Zamu samu cikakkun bayanai akan hakan domin kuwa, ba wata matsala ce da zata faskara wajen shawo kanta ba, zamu hada karfi da karfe don dai-dai ta al’amuran.
Tambaya: Me zaka ce akan ma’aikatan KRPC?
Adewale: A bisa baya nan da na samu, ma’aikata ne hazikai kuma na gari kuma suna iya kokarin wajen ganin ci gaban kamfanin, saboda haka ni da su za mu tsaya tsayin daka don yin aiki tukuru a kamfanin.
Mun Gode.
Nima Na Gode.