Yusuf Shuaibu" />

Matatun Man Dangote Za Su karfafa Darajar Naira Da Ceto Tattalin Arziki – Majalisar Wakilai

Majalisar Wakilan Nijeriya ta bayyana cewa, matatan man kamfanin Dangote zai karfafa darajar kudin Nijeriya da kuma ceto tattalin arziki idan aka samu nasarar kammalawa. Majalisar ta bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da wakilan majalisar suka ziyarci matatan man kamfanin Dangote wanda ake gudanar da ke yankin Ibeju Lekki ta Jihar Legas.

Shugaban kwamitin majalisa a kan albarkatun kamfanonin mai, Hon. Sabo Nakuda, ya ce, “akwai sabra doka da za a samar a kan kamfanonin mai, mun ziyarci dukkan sauran matatun mai ba wai matatan man Daangote muna ziyarta ba kadai.
“Jiya mun ziyarci matatan mai na Kaduna. Za mu je matatan mai na Fatakwal da na Warri, saboda mu san takaitacce bayanai da kuma abubuwan da ya kamata a yi wajen samar da dokan da zai taimaka wa matatun man su ci gaba da aiki yadda ya dace,” inji shi.
Ya kara da cewa, ziyarar da muka kawo matatan man kamfanin Dangote ya yi matukar ba mu mamaki. Ya ce, idan muka duba yadda aka zuba jari, wannan abun mamaki ne mutum ya gudanar da irin wannan aiki a lokacin da tattalin arziki yake samun matsaloli.
Nakuda ya ci gaba da cewa, bayan samar da ayyukan yi da wannan aiki zai yi, ana mai tabbaci cewa an gudanar da wannan matata a daidai lokacin da ya kamata, domin zai karfafa naira saboda muka kashe miliyoyin daloli kafin mu sami nasarar shigowa da mai cikin kasar nan. Ya ce, majalisar kasa za ta bai wa wannan aiki goyan baya dari bisa dari.
“Idan muka kasa taimakon wannan matatan ma na kamfani Dangote, to kamar mun kasa taimakon tattalin arzikin Nijeriya ne,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, ‘yan majalisa suna aiki kafada da kafada domin tabbatar da cewa an samu amincewa da dokokin da za su tallafa wa kamfanonin mai daga nan zuwa watanni biyu masu zuwa.
Shi ma shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai, Mista Mohammed Monguno ya yaba kamfanin Dangote bisa narkar da wannan gagarumin aiki na matatan mai. Ya bayyana cewa, wannan matatan mai zai yi matukar farfado da tattalin arziki wajen gudanar da saye da sayarwa na mai a cikin kasar nan.
Ya ce, “majalisar kasa za ta tabbatar da an amince da wannan doka wanda zai tallafa wa masu zuba jari a bangaren kamfanonin mai da gas, domin a samu gasa wajen zuba jari a cikin kasar nan,” inji shi.
Shugaban gudanar da tsare-tsare na kamfanin Dangote, Mista Debakumar Edwin, ya bayyana cewa, idan an samu nasarar kammala wannan matata, za ta dunga tace gangan danyan mai guda 650,000 a kowacce rana wanda za ta iya gamsar da kashi 100 na bukatar man fetur a Nijeriya tare da saukaka shigo da mai a kasar nan.

Exit mobile version