Daga Bilkisu Ibrahim
Ilimi gishirin rayuwa hakika duk wanda ya samu ingantaccen ilimi zai samu saukin abubuwa da yawa game da wannan rayuwar da muke ciki, domin kuwa kasancewar sa na mai ilimi zai dinga sa shi a dukkan al’amura na rayuwarsa.
Hakan zai sa ya samu mafita da sauki akan duk wani abu daya tunkara tare da samun dimbin nasarori akansa daga karshe. Amfanin ilimi game da rayuwar dan Adam baya misiltuwa, domin kuwa shi ilimi fitila ce da ke yaye duhu, magani ne da ke warkar da ciwo, mafita ce daga dukkan bakin ciki da damuwa.
Kasancewar samun ilimi ba karamin tasiri yake ba wajen gyara rayuwa da tsamo mutum daga duhu na jahilci, ya zama wajibi akan iyaye, shuwagabanni da al’umma gaba daya su dukufa wajen tabbatar da samun ingantaccen ilimi wa al’ummansu, musamman mata.
Samar wa yara mata ingantaccen ilimi nada matukar alfanu wajen cigaban al’umma gaba dayanta, domin kuwa mace ita ce malama ta farko a rayuwar mutum, idan har yakasance ma’abuciyar ilimi ce, to babu shakka za ta samar wa da al’umma nagartattun yara da za su zama abubuwan alfari da tunkaho.
Akasarin manyan malamai magabata irinsu Imamu Malik da sauransu, kasancewar iyayen su mata ko kuma wadanda suka yi mu’amala da su mata ne masu ilimi hakan ne ya jawo musu wannan shahara da suka samu a duniya da har yau har kuma gaban gobe ana cin amfanin ilimin da suka samu waje mata.
Duba ga wannan da kuma sauran misalai irin nasu Nana Asma’u Usmanu Danfodiyo yadda ta bayar da gagarumar gudunmawa a harkar ilimi ta hanyar rubuce rubucenta wadda a kasar Hausa har yanzu ba’a samu makamanciyarta ba ya zama wajibi akan wannan al’umma ta dage damtse domin tabbatar da sama wa yara mata ilimi ta haryar bari su shiga makaranta da kuma tilasta ma iyayen su barinsu su gama makaranta akallah sakandare kafin a aurar dasu.
Matsalar cire yara mata daga makarantun sakandire domin aurar dasu yayi kamari sosai a wannan yankin namu na Arewa.domin kuwa a wani binkice da muka gudanar a wasu Makarantu a Zaria alkaluma sun nuna a cikin kashi 💯% na yara mata da suke fara karamar sakandire JS1, kashi 40% ne kawai suke rubuta jarabawar kammala Sakandire ta SSCE ba’a aurar dasu ba.
Jahilci ciwo ne wanda ke dauwamar da al’umma cikin duhu na talauci da rashin sanin makama.
Kamar misalin yaran da’a ke magana akan su, suna JSS, SS1 basu gama islamiyya ba duk an aurar da su. Sun fara karatu basu gama ba suna da yawa sosai acikin al’umma. Da zarar ta yi aure tafara zuba yara wata ma duk shekara take haihuwa kankace kwabo ‘yar shekara 18 ta koma tamkar tsohuwa bata san yanda za ta kula da kanta ba balle lafiyanta dana yayanta, tsaftace mahalli ma sai a hankali.
Irin wadannan yaran makomar rayuwar su takan kasance sai a hankali, saboda rashin samun ingantaccen ililmi na addini dana zamani. Babbar matsalar ma ita ce ba lallai bane wadanda aka basu auren nasu, su maida hankali wajen koyar dasu ko sama musu wadanda zasu koya musu ilimin addini.
Zaka ga ana Rayuwa ce kara zube, babban abunda aka tasa a gaba shi ne yadda za a samu abun masarufi asa a bakin salati basa kokarin neman ilimin dazai inganta rayuwar su dana yayansu anan duniya da kuma gobe kiyama.
Duba da haka lallai ya zama wajibi ga hukumomi su samar da wani tsari wanda zai tabbatar da yarinya naci gaba da karatunta koda kuwa an mata aure ne.
Mutane musamman, shuwagabanni al’umma da malamai su taimaka ma hukumomi wajen wayar wa al’umma kai domin su fahimci muhimmanci da alfanun haka.
Allah ya mana gudunmawa, Amin.