Abdullahi Muhammad Sheka" />

Matsalar Cinkoso A Gidajen Yari: Ganduje Ya ‘Yanta Fursunoni 2,517 A Shekara Hudu

A kokarin da Gwamnatin tarayya ke yi na ci gaba da rage cunkoso a gidajen Yari da kuma kyautata harkokin shari’a a fadin kasar nan baki daya, Gwamnatin Jihar  Kano, karkashin jagoranci Dakta

Abdullahi Umar Ganduje, ta yi nata hodasar inda ta ‘yanto kimanin Fursunoni 2,517, a cikin shekaru hudu kacal.

Gwamna Kanon, ya bayyana haka ne a daidai lokacin da ya kai ziyararsa ta Sallah gidan Yarin da ke Goron Dutse, bayan sake ‘yanta wasu Fursunoni guda 200 a kan kudi sama da Naira Milyan 1.5.

“Mun fitar da wadannan Fursunoni bayan cika ka’idojin da Hukumar shari’a ta kasa ta tsara, mun kuma yi haka ne bisa umarnin da aka baiwa Gwamnoni domin taimaka wa wajen rage cinkoso a wadannan gidaje na Yari.

Wasu daga cikin muhimman ka’idojin da ake cikawa kafin fitar da wadannan daurarru su ne, matsalar tara ga wadanda suka kasa biya,

matsalar rashin lafiya , tsufa da kuma wadanda aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya ya kasance yanzu kuma sun yi raun kwarai da gaske bisa hukuncin kisan da aka yanke musu”, in ji gwamnan.

Daga nan kuma, sai gwamnan ya shawarci wadanda suka shaki iskar

‘yancin da su kasance cikin masu kyakkyawar tarbiyya don amfanin kansu da kuma sauran al’umma baki daya. Sannan ya sake yi musu fatan zama nagartattu kuma ‘Yan kasa na gari wadanda za su taimaka wajen inganta harakokin tattalin arziki tare da ci gaban siyasa a wannan jiha da ma kasa baki daya, in ji shi.

Har ila yau, daga cikin mutane 200 da aka ‘yantar din, guda 60 sun fito daga gidan Kurkukun Kurmawa ne, 33 daga Kurkukun Wudil sai kuma cikon 107,  su kuma daga daga sauran gidajen Yarin da ke fadin wannan jihar daban-daban. Sannan kuma ya tabbatarwa da sauran masu zama a gidan kason da cewa, nan da watanni biyu musamman a lokacin bikin babbar Sallah, za su tabbatar da ganin wasu karin daurarrun sun karasamun da shakar iskar ‘yancin.

A gefe guda kuma, DCP Yahuza Aliyu ne ya gabatar da jawabi a lokacin taron, inda ya jinjina wa Gwamnan bisa wannan kabakin alherin da

gwamnatin tasa ta kwarara a cikin shekaru hudu da suka gabata. Haka nan, a cewar tasa  wannan ‘yanta Fursunoni da gwamnan ya yi a yau, na nuni da tabbacin cewa su ma wasu Fursunonin na nan tafe nan ba da jimawa ba.

Bugu da kari, gwamnan Kanon ya sake kai irin wannan ziyara ta musamman gidan yara kangararru da ke Goron Dutse. Inda a nan ma gwamnan bayan cika dukkanin ka’idoji ya sake fitar da yara 9, bayan biya musu nauyin da ke wuyansu. Kazalika, ya sake tabbatar da ci gaba da yin kokari wajen samar da abubuwan da ake bukata musamman a bangaren samar da kayan koyar da sana’o’i ga yaran da ke tsare a wannan gida.

Haka kuma a gidan Marayu na Nassarawa, nan ma gwamnan ya yi alkawarin inganta  harkokin jin dadin yaran da ke wannan gida. Sannan  ya kara da cewa, shi fa da na kowa ne, in ji Ganduje.

Kafin Gwamna Ganduje ya kai wannan ziyara sai da ya halarci sallar

idin Karamar Sallah, wadda aka gudanar a filin Idi da ke kofar Mata

lokacin da Mai Martaba Sarkin Kano, ya jagorancin Sallar idin ya kuma

bukaci kokarin samar da tabbatacin tsaro a cikin hudubar tasa. Sarkin ya kuma sake yin kira ga jama’a da su hada hannu da gwamnati domin inganta harkar tsaro a kasa baki daya, in ji Sarki.

A lokacin Sallar idin, Gwamna Ganduje na tare da Mataimakinsa Nasiru

Yusif Gawuna, Shugabannin bangarorin tsaro, Shugabannin Jam’iyya, ‘Yan Majalisar Wakilai da na Dattijai da kuma manya-manyan Shugabannin sassan ma’aikatun Gwamnatin Kano.

Wakazalika, Bayan idar da Sallar idin  gwamnan da ‘yan tawagarsa suka koma Fadar gwamnatin, inda aka gudanar walimar cin abinci a dakin taro na Afrika House, Gwamnan Kanon ya taya daukacin al’ummar jihar murnar kammala azumin watan Ramadan. Ya kuma tabbatarwa da jama’a Kano cewa, gwamnatinsa za ta yi aiki da jama’a daga

bangaren jam’iyyun adawa a wannan jiha.

Daga nan ne kuma, ya sake yin tsokaci a kan wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin tasa ta samu a cikin shekaru hudu, ya kuma jaddada cewa zangonsa na biyu, da yardar Allah sai ya fi na farko wajen samar wa da al’ummar wannan jiha ayyukan alheri.

Haka nan, wani gwaggwaban aikin alheri da Gwamna Gandujen ya gudanar jim kadan bayan Sallar idin bana nan shi ne, ziyartar makabartar Goron Dutse. Inda aka gudanar da addu’o’i na musamman ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya tare da nema masu gafarar Allah.

Mai magana da yawun Fadar Gwamnatin Kanon ne, Malam Abba Anwar ya Shaida wa Jaridar Leadership A yau.

Exit mobile version