Matsalar Ilimi Daga Tushe: Yawancin Masu Shigowa Jami’a Ba Su Cancanta Ba —Farfesa Kabir

Ilimi

…Sannan Ana Yaye Su Ba Su Dahu Ba

– Jami’o’i Masu Zaman Kansu Na Da Hannu A Rugujewar Ilimin

 

Farfesa na farko a fannin ilimin tarihin abin da ke karkashin kasa (Archeology) a yankin arewacin Nijeriya kuma tsohon shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), reshen Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, FARFESA MUHAMMAD KABIR ALIYU, ya yi bayanai da dama game da matsalar tabarbarewar ilimi a Nijeriya wanda ya nunar da cewa an bar gini ne tun ran zane. Sai dai ta kaka? Ya bayar da amsoshi a hirarsa da Mataimakin Editanmu BELLO HAMZA:

 

 

Masu karatu za su so ka fara da gabatar da kanka…

 

Sunana Farfesa Muhammad Kabir Aliyu, ina koyarwa a nan Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, kuma ni ne Editan Mujallar Education Monitor, kuma ni tsohon Shugaban Kungiyar Malamai ne ta Jami’o’i (ASUU), a nan reshen Jami’ar Ahmadu Bello.

Kasancewarka Editan jaridar da take kula da sashen ilimi na musamman wadanne abubuwa kuka gano a kan halin da ilimi ke ciki a kasar nan?

 

A gaskiya akwai matsaloli da yawa da muka gani, na daya ba kawai don muna buga wannan jarida ba, a’a, don ma dadewar da muka yi a cikin jami’a bangaren ilimi musamman ma a jami’a. Babbar matsala ta farko da muke samu ita ce yadda ilimin ma gaba daya tun daga firamare ba wai nan jami’a ba, zuwa sakandire, irin su makarantun Fasaha, Kwalejin Horon Malamai, zuwa nan jami’a, gwamnati ba ta dauki ilimin da muhummancin da ya kamata ta dauke shi ba.

Me ya sa musamman a mataki na farko da na biyu, firamare da sakandire, daga nan ake barin shirin?

Su yara tun suna kanana ake shirya su yadda ya kamata, mataki ne mai kyau, kamar yadda turawa ke cewa idan aka ba su ‘background’ mai kyau, yakan sa ko da sun zo jami’o’i sai ka ga karatun nasu ya yi kyau kuma ya yi karko.

To amma sai muka lura cewa mafi yawan wadanda suke shigowa jami’o’i a yanzu ba su cancanta ma su shigo jami’o’i ba saboda ba a shirya su sosai tun daga firamare zuwa sikandire ba. Za ka ga mafi yawa sukan zo a danyensu ne kawai, to mafi yawa mu ne mukan dan gyaggyara su, kuma kafin shekara hudu sai a ce sun gama, saboda haka yanzu har mutane sukan ce yanzu muna fitar da dalibai wadanda ake ce masu ‘Half baked’, wato wadanda ba su dahu sosai ba, ba su kware ba, wannan na daya kenan. Na biyu su kansu ma malaman jami’ar za ka ga akwai da yawa wadanda ba su kware ma sosai ba wajen koyarwa a jami’o’in. Kuma abin da ya sa ba yau ya fara ba, duk kuma laifin gwamnati ne, saboda gwamnati ba ta dauki muhimmaci ta ba ilimin sosai ba ta yadda su malaman za a kula da su.

Sai da yawan masu ilimin, masu kwazon suka bar jami’o’i, aka rika barin wadanda ma ba su cancanta ba suna shigowa jami’o’i a hankali a hankali, sai ya kasance kamar mutane suna zuwa ne kawai in sun rasa aikin yi, to shi ya sa ka ga kungiyarmu daga baya muka tashi tsaye muna cewa wannan ba zai yiwu ba, ana ta yajin aiki muna cewa gwamnati ta kara kudi, a kula da malamai.

Duk wannan yakin da muka yi ta yi, ni dai ina ciki fiye da shekara 30, to a hankali a hankali saboda wannan kwazon da muka yi muka tashi tsaye muna gaya wa gwamnati abin fa ba zai yiwu ba; na daya ta kula da malamai, na biyu ta karo kayan aiki, su daliban kansu ma a kula da su, wurin da za su zauna, wurin da za su yi karatu, dakunan da za su yi bincike to a hankali dai gwamnati ta fara sauraronmu har aka fara gyarawa, aka ma fara gyara albashin malaman, daga baya a hankali a hankali har malaman da suke da kwazon suka fara dawowa, amma mu a yadda muke gani har yanzu akwai sauran gyaran saboda duk wata kasa fa da ka gani a duniya ci gabanta daidai yake da ci gaban iliminta, ba za ta iya wucewa ba. Ba Nijeriya kawai ne ba, in ka bar ilimi a kasa haka kuma za ku zauna a kasa, in iliminku ya yi sama haka kuma za ku yi sama na biyu kenan.

To akwai kuma su kansu iyaye, sai muka lura cewa su kansu iyaye ba su damu da wane halin da ‘ya’yansu ke ciki a makarantun ba, Idan kawai uba ya samar wa dansa gurbi a makaranta ya yi rijista kawai sai ya manta da shi, ya ya ke kwana, ana ma koya mashi, akwai dakunan karatu? A’a ba abin da ya dame su don ni ban taba jin ma kungiyar iyaye ta jami’a a ce suna sa ido su ma, to ka ga idan malamai suka yi kuka za ka san cewa eh gaskiya ne, to amma sai ka ga idan malamai suka yi kuka sai ka ga iyayen ma suna zaginmu saboda ba su san abin da ke faruwa a cikin jami’o’in ba, kuma za ka ga duk duniya haka ake yi, za ka ga da malamai ne da gwamnati da iyaye ake haduwa a samar da ci gaba ga ilimi a kasa, to a takaice dai abin da muka lura kenan yanzu.

 

Ka yi maganar yajin aiki da ake ta yi, to mece ce mahangarka a kan wannan matsalar da ake ciki ta gwamnati da kungiyar ASUU, ya za a yi a fita daga cikin wannan dambarwa?

 

Na farko sai ita gwamnatin ta yarda akwai matsala a cikin harkar ilimin, matukar gwamnati ba ta yarda ba kuma ta ci gaba da sanya siyasa a cikin harkar ilimi, to ba za a taba zama lafiya tsakanin gwamnati da malaman jami’o’i ba. Domin makarantun nan fa ba na malaman jami’o’i ba ne, makarantun nan na ‘yan Nijeriya ne, su kansu wadanda suke shugabancin ‘yan Nijeriya ne, mu kuma masu ‘yanci ne, aikinsu ne su kula da ilimin nan saboda kowa ya amfana su ma su amfana. Sai muka ga ita gwamnati sai tana siyasantar da abin, in muka ce mata abu kaza ba shi da kyau, a gyara kaza sai su yarda kawai don saboda a zauna lafiya, muna komawa aiki sai su manta da shi, kodayaushe haka ake yi, in ka ji ana yajin aiki nan a sake dawowa, za su zauna a yi yarjejeniya da su a ce kaza su yarda, a ce kaza su yarda, ku yi kaza su yarda, don duk mu koma aiki saboda mu aiki muka zo yi, to ana komawa aiki sai su manta da ku, a yi ta magana, mu yi ta magana sai su ki yi, sai ka ga an sake komawa yajin aiki. “So” dole sai gwamnati ta sa kula a kan harkar ilimin nan su yi alkawarin gaskiya kuma su cika alkawarin, to za ka ga wannan yajin aikin zai bace.

 

Ya za ka dora yanayin cin hanci da rashawa a manyan makarantun kasar nan?

 

Maganar cin hanci da rashawa akwai shi a cikin jami’o’i, saboda me, su jami’o’in nan a cikin Nijeriya suke wadanda ke cikin jami’o’in nan ‘yan Nijeriya ne, to duk abin da ke faruwa a waje yana shafar na ciki saboda su ma ‘yan Nijeriya ne kuma suna ganin abin da ke faruwa, mafi yawa za ka ga suna ganin abin da ‘yan siyasa ke yi, musamman ma shugabannin suna ganin abin da ‘yan siyasa ke yi su ma suna yi wajen ba da kwangila, da wurin abin da ake cewa ‘Kick back’ wajen karbar ba da kwangilar duk ana yi, wurin daukar aiki ne duk yana faruwa amma ba zan ce maka a ko ina a kowanne sashe ba amma dai yana faruwa saboda me ai akwai ma shugabannin jami’o’i da aka ma kulle saboda an ji abin da suka yi, akwai wadanda ma aka kulle su. To ka ga yana faruwa kenan, “so” ban da shugabannin ma za ka samu yana faruwa kadan-kadan ana kama wasu kuma har a kore su a aiki, yana faruwa.

 

Yaya alakar malamai da dalibai a jami’o’inmu musamman ganin irin abubuwan fallasa da ke fitowa na badala da abubuwa kamar haka?

Gaskiya ne tsakanin malamai da dalibai ana samun matsaloli wani lokaci, saboda kamar yadda na fada maka matsalar cin hanci da rashawa ko shi ma wannan matsalar ta a samu batagari a cikin malamai akwai su, wanda za ka ga su ba abin da suke yi sai lalata yara ko karbar kudi a hannun yara a biya su su gyara wata jarabawa, amma za ka ga ba su fi kashi 5 a cikin 100 ba, amma ka san an ce wake daya shi ke bata gari. Kamar a nan jami’ar na san an kori malamai, an kama su kuma an kore su, ba za ka iya raba al’umma da bata gari ba ko da kashi 1 ne, “so” akwai su.

 

Bayani ya nuna cewa kai ne Farfesa na farko a sashen Arewa a bangaren da ya shafi kimiyyar tarihi wadda aka fi sani da ‘Archaeology’, ya ka samu nasarar haka?

 

Allah ne ya so kasancewar haka, ba wai ni ne na shirya haka ba ko wani ne ya shirya haka, Archaeology kamar yadda ka ce kimiyyar tarihi na duniya, kamar bako ne a Nijeriya bai dade kamar yadda sauran fannoni ba, to ko a duniya ma haka ne, kamar su ‘yan Kudu sun fara yi don an samu Farfesa masu yawa ma kafin a soma yi a nan, to nan ‘yan Arewa akwai malamai na ‘yan Arewan sai dai ba su zama Farfesa ba.

To ni dai cikin ikon Allah a shekarar 2012 Allah ya sa na zama Farfesa na farko a nan Jami’ar ABU, wanda yake a wannan sashen na ‘Archaeology’, na yi kwazona, na yi karatuna na yi rubuce-rubucena cikin ikon Allah ita jami’a ta duba ta ga na cancanta aka ba ni Farfesa.

 

Kwanakin baya kungiyar ASUU ta yi wani taro a Bauchi, inda ta fitar da bayanin cewa ya kamata a dakatar da yadda ake fita karatu kasashen waje, wasu kuma na ganin ya kamata ASUU ta ja wa kanta linzami a kan yawan yajin aikin da take shiga, me za ka ce a kan wannan dambarwa?

 

Allah kadai ya san yadda za a warware wannan dambarwar, ka san su ‘yan siyasa da suke da halin samun kudi ko ta halal ne ko ba ta halal ba ne, su suna da halin daukar ‘ya’yansu su kai waje, amma dalilinsu ba wai kawai yajin aiki ba ne, in yajin aiki ne suna da ikon su hana yajin aikin, su ke mulki da kudi, matsalolin da muke cewa din a duba a gani da gaske ne matsalolin in aka ga da gaske ne, in aka gyara ba za mu rika yajin aiki ba, a mai da jami’o’inmu kamar yadda jami’o’i suke a duniya, haka muke so.

In aka gyara zai hana yajin aiki, idan aka daina yajin aiki zai hana mutane su rika daukar ‘ya ‘yansu suna kaiwa waje, mu mun tabbatar cewa idan aka gyara wannan matsalolin za a daina yajin aiki to zai yiwu kuma a daina daukar yara ana kai su kasashen waje.

 

Shin akwai wani abu da kake son fada na karin haske ga jama’a da ba mu tambaye ka ba?

 

Ka yi tambayar kusan duka amma abin da nake so mutane su sani shi ne, ci gaban ilimi na kowacce kasa a duniya, ya kamata a ce mu Nijeriya muna daga cikin kasashen duniya manya. Duk yadda ka dauki kasashen duniya da matsalolinmu a duniya muna daga cikin kasashen da ba za a iya ture su gefe ba, amma yadda muke kula da iliminmu abin kunya ne a ce a kasafin kudi sai mu ba da kashi 7, kashi 5, kashi 6 maimakon an ce akalla mu ba da kashi 26 ne, amma muna ba da kashi 7, in mun ba da da yawa kashi 9 fiye da shekaru 20 da na sani.

To duk yadda ka yi wannan kuwa ba yadda za a yi mu ci gaba sai dai mu yi ta maneji haka nan. Mutane su san wannan ba wai muna fada ne ba a’a, mutane su je su duba su gani, nawa Nijeriya take sawa a kasonta na kasafin kudi nawa ake sawa bangaren ilimi.

Bai wuce kashi 10 ba, to kuma a duk duniya an ce duk kasar da ba ta ba da kashi 26 ba a ilimi dai to ba za ta ci gaba ba, to kuma na ce maka in kuma ilimin bai ci gaba ba, ba yadda za a yi ta ci gaba, yawan da iliminka ya kai haka ma ci gabanka.

Abin da nake cewa shi ne su wadannan jami’o’in da ake ce masu masu zaman kansu kasuwanci fa suke yi, so suke su zo a ce an ba su kudi su ce sun ba yara karatu, yanzu za ka ga a wadannan jami’o’in, mafi yawansu za ka ga ba yadda za a yi yaro wai ya shiga aji ka ga ya fadi, ko da bai san komai ba. Ka je ka biya Naira 500,000 a ‘Term’ ko a ‘Semester’ ga yaronka a shekara ka biya 1,000,000 akalla kenan, yaya za a yi a zo a ce maka ya fadi ko da kuwa bai san komai ba, Malami ya yi karatu yaro ya fadi ya kayar da shi sai shugaba ya kira shi ya canza, duk suna yi, to suna daga cikin wadanda ma suke kara rushe ilimin Nijeriya.

Exit mobile version