Na dade Ina nazari dangane da irin yadda matsalar karancin ruwan fanfo a birnin Sakkwato ta azzara, mussaman ga yadda lamarin ya koma na rashin sanin hanyar bullo ma matsalar da neman ko da akwai wata hanyar rage wannan lamarin ko magance ta bakidaya; tun ma ba daga ita kanta Hukumar Kula da Samar da Ruwan Sha ta jahar Sokoto har ya zuwa ga Ma’aikatar Ruwa da albarkatunsu ba.
Abin ban takaici ganin cewar lamarin ya fara daga matsalar da ake iya yiwa jama’a bayani har ya azzara zuwa fiye da kwanaki 60 a na cigaba da fuskantar wahala da rashin sanin makoma, kamin sa’ilin gwamnati ta fara nuna damuwa ko daukar mataki akan wannan matsalar.
Shi kanshi kwamishinan da ke kula da ma’aikatar ruwa, Alhaji Muhammadu Arzika Tureta, ya ja bakinsa ya tsuke, har lokacin da masu sharhi a shafin zumunta na Facebook da kafofin yada labarai na rediyo su ka fara tattauna matsalar da yin korafi a kan sakaci da wannan lamarin kamin ya fito ya yi bayani a kan dalilan karancin ruwan ga al’ummmar Sakkwatawa.
Karancin ruwan sha a birnin Sakkwato, musamman irin wannan lokacin ba wani sabon abu ba ne ga masana, duk da ya ke an dade a na samun irin haka daga matsalolin lalacewar injunan tace da tura ruwan sha zuwa ga manyan bututun da ke kai ruwan a unguwanni da mahadar rarraba su, a kan danganta matsalar daga karancin wutar lantarki ko karancin magungunan da a ke amfani da su wurin tace ruwa ko yawaitar matsalolin turo ruwa daga babban dam na Goronyo ko gulaben Rima.
Matsalar Dumamar Yanayi Da Kuskuren Nimet
Ga bayanin da gwamnatin jahar Sokoto ta yi, wannan matsalar karancin ruwan sha ba daga laifinta ba ne, don kuwa da ma a na dogara ga samun ruwan da za a rarraba ma al’umma daga babban dam din Goronyo da ke da yawan ruwa da tun farko a ke turawa zuwa Kogin Rima da sauran kananan gulabe; musamman wadanda a ke kwasar ruwan zuwa babban bututun da Hukumar ruwan sha ta hada don kaiwa ga mahadar da a ke tace su zuwa ga jama’a.
Wannan dam din ya na da karfin ajiye ruwa har kubik mita miliyan dari tara da arba’in (940,000,000 cubic meter) wadanda cikinsu a ke baiwa manoman rani da kuma wasu a jahar Kebbi don gudanar da ayyukan noman rani.
Da ya ke a baya an yi wasa da lamarin bayan Hukumar Kula da Yanayi ta kasa, NIMET ta yi gargadi a kan yiyuwar samun ruwan sama masu yawa da zasu yi barazana da janyo matsala ga dam din, lamarin da ya janyo bayar da umurni rage yawan ruwan da toshe hanyoyin shigowarsu zuwa ga dam tare da bude hanyoyin fitarsu a nan take.
A cikin haka ne a ka fuskanci matsalar dumamar yanayi wanda ya kawo karancin ruwan sama a wasu sassa masu yawa, har ma da ruwan da ke zuwa ga dam din, don ko ya dogara ga samun ruwan nasa ta wasu mahadar ruwan daga gulabe masu yawa.
Hakan ya sanya ruwan na dam din su ka yi karanci ga samarwa manoma rani da wasu yankunnan da a ke tura su da issasun ruwa, abin da ya janyo karanci da yawan bukata ga lamuran noman rani da baiwa jama’a ruwan da zasu sha.
Sakamakon bayanin hukumar NIMET inji hujjojin gwamnati, hakan ya janyo an bar Dam din na Goronyo da karancin ruwa wadanda ba su zarce akalla kubik mita guda miliyan dari ba (100, 000, 000 cubic meters). Wannan lamarin ya janyo karancin ruwa ga wasu ayyuka da a ke yi ta amfani da dam din tare da rage karfin ruwan da za su je ga wasu sassa da su ka dogara da ruwan, mussaman gulaben da su ke tsotsa ruwa da kaisu mahadar kogin Rima don baiwa Sakkwato ruwan sha.
Sai dai duk da hasarar kusan kubic miliyan dari takwas (840,000,000 cubic meters) bai janyo hankalin gwamnatin jahar Sokoto ta hannun hukumar samar da ruwan sha da wuri-wuri ba, don daukar mataki na gaggawa watanni har kusan hudu da fara fusknatar karancin ruwan da ke zuwa a ainihin manyan tankunan ajiye ruwa na hukumar da ke gidan ruwa ba.
Wannan shi ne babban sakaci da rashin kulawa da hukumar ruwan sha da masu lura da ayyukan samar da ruwan su ka yi; abin da ya janyo yanzu mafi rinjayen jama’a na cikin masifar karancin ruwan sha da na amfani a wurare daban-daban na birnin Sakkwato da kewaye.
Kusan a farkon lokaci na gyara da sake tsarin hanyoyin tace da rarraba ruwan sha ga al’ummar Sakkwato, an bayyana a na bukatar kusan galan miliyan biyu zuwa uku kowace rana na ruwan sha ga birnin na Sakkwato da kewaye, abin da ya janyo habaka na bukatar ruwa don amfanin yau da kullum.
Hukumar ruwan sha din da a ke ganin tana fuskantar karancin kwarrarun masana da ma’aikata a kan fanin ruwa da bincike ta koma tamkar wurin zaman hira da jiran tallafin gwamnati, don kuwa kudaden shiga na sayar da ruwan sha din bai iya gudanar mata da ayyukanta koda kuwa na mako biyu.
Makudan Kudade Babu Amfani A Fili?
Wani bayani maras tabbas daga wata majiya ya baiyana a kusan kowane wata gwamnatin jahar Sokoto ta na fitar da zunzurutun kudade har Naira miliyan dari da saba’in da shida (N176,000,000) wajen gyara da tace ruwa tare da biyan kudaden wutar lantarki da na ayyukan mussaman ga hukumar samar da ruwan sha wadda bata wuce tara Naira miliyan arba’in (N40,000,000) na kudaden ruwa a shekara ba.
Wadanan kudaden ba su cikin na biyan magunguna da wasu ayyukan musamman na shekara shekara, inji majiyar.
Hakika sakaci da rashin kulawa na hukumar tare da hadin gwiwar ma’aikatar samar da ruwa na daga cikin dalilan da yanzu ya janyo al’umma su ka fada cikin wannan wahalar ta karancin ruwan sha, fiye da irinsa a kusan tarihin samar da ruwan sha a jahar Sokoto.
Rijiyoyin Burtsatse
A watanin baya a ka bayar da rahoton bayar da kwangilar gina rijiyoyin burtsatse irin na zamani har guda 150, sai dai tun lokacin har yanzu babu labarin guda nawa a ka gina ko a daya daga cikin yankunan da su ka fi shan wahalar ruwan sha na birnin Sokoto.
Da a ce an kammala wadanan rijiyoyin cikin lokaci zuwa yanzu da al’ummar Sakkwatawa ba su koka a kan matsalar karancinå hanyoyin samun ruwa a gidajensu ko yadda zasu samu ruwan na sha ba.
Tsarin da gwamnatin ta ke son bi a yanzu na sake gyara da bunkasa rijiyoyin tuka-tuka ko na hannu har guda 79 zai rage radadin ne na dan lokaci, amma muhimmin abu shi ne a yi gyaran da zai dore a cikin lokaci muddin a na son kawo karshen karancin ruwa bakidaya.
Mafita
Haka ma akwai bukatar kulawa ga amfani da tankoki na mota a cikin birnin Sakkwato da kewaye don rarraba ruwa tamkar irin yadda gwamnatin jahar Zamfara tayi amfani da shi da a ka samu mummunan matsalar ruwan sha a dam din wanke da ke bayar da ruwa ga garin Gusau.
Sai kuma sake gyara da inganta manyan tankokin ajiye ruwa wadanda a ka gina a lokacin gwamnatin Attahiru Bafarawa a tsohuwar kasuwa don ajiye da kuma tura ruwan da al’umma su ke bukata.
Akwai bukatar a kusan kowane wata akwai akalla galan na ruwa har miliyan 270 ga wadanan tankunan don taimakawa samar da issasun ruwa ga birnin na Sakkwato. Haka ma tankokin da ke Ali Akilu na bukatar kulawa, don inganta ajiye ruwan da zai amfani kusan manyan ungunwanin da yanzu haka su ke cikin bukata.
Sai kuma fito da hanyar bunkasa aikin ruwa na Asari wanda tsohon gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi, don kara yawan hanyoyin da jama’a za su amfana ga ruwan sha.
Kalubalen Da Ke Gaban Gwamna
Wani abin damuwa shi ne lokaci ya yi da gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal zai zage damtse wajen ganin ya fito da tsare-tsare na gyara ga hukumar samar da ruwan sha da ita kanta ma’aikatar ruwan ta yadda za a baiwa masana damar shigowa su bayar da gudumuwarsu.
Gwamna Tambuwal ya sani ya na da aiki mai yawa a kan wannan lamarin, don kuwa duk matsalar da za a fuskanta a jahar Sokoto, ta na da sauki bisa ga matsalar ruwan sha da lamarin tsaro. Da ya ke lamari tsaro bai da barazana a yanzu, ya dace ya mayar da hankali ga hanyoyin bunkasa samar da ruwan sha ga al’ummarsa.
Ko A Na Yiwa Gwamna Zagon Kasa Ne?
Masu yi ma sa zagon kasa da wadanda a ke ganin su na murna ga faruwar wadannan wahalolin, ya dace ya dauki mataki na karshe a kan lamarin. Ya sani fa muddin zai iya gyara, to kuwa za a rage wahala ko kuma ya cigaba da fuskantar rashin amincewa daga al’ummar da ke wahala daga wannan masifar.
Ya dace ta kasance muhimmin darasi da kalubale gare shi da duk wadanda ke da alhakin kulawa da samar da ruwan sha ga al’umma. Ta haka zai taimaka a kawo karshen wadannan wahalhalu da su ka janyo koma-baya ga karatun dalibai da yiwa rayukan al’umma barazana da irin cuttutukan da a ke gani na iya bulla idan a ka cigaba a haka,
Ruwa abokin rayuwa, ya na da kyau gwamnati ta yi hobbasa ga ganin lamarin ya zama sauki.
Yusuf Dingyadi dan jarida ne mai zaman kansa a birnin Sakkwato