Daga Muhammad Maitela,
Biyo bayan katsewar layin wutar lantarki a wasu garuruwa, wanda aranar Alhamis Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kai ziyara a ofishin ministan makamashi, Engr. Saleh Mamman da ke Abuja, domin tattauna batun hanzarta aikin sake gyaran wutar da ta hada Damaturu zuwa Maiduguri wanda hare-haren mayakan Boko Haram ya shafa.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa mayakan sun katse wutar yankin ta hanyar amfani da abubuwa masu fashewa, al’amarin da ya jefa dimbin jama’ar Maiduguri zama cikin duhu na kimanin tsawon wata guda, kuma hakan ya faru ne ta dalilin wasu hanyoyin wuta guda biyu da suka samu tankarda a yankin.
“Wannan matsalar katsewar wutar ta doshi wata guda jama’ar Maiduguri su na rayuwa a cikin duhu. Wanda bisa ga hakan ne a hukumance muka kawo muku ziyara domin karfafa wa tare da bayyana bukatarmu ga ofishin ku domin daukar matakin gaggawa dangane da aikin sake gyara wutar, kuma gwamnatin jihar Borno za ta yi duk abinda ya dace wajen bayar da cikakken goyon bayan wannan aiki.” In ji Zulum.
A hannu guda kuma, Gwamna Zulum ya bukaci taimakon gwamnatin tarayya wajen samar da layukan wuta masu amfani da hasken rana, musamman a birane da yankunan karkara a jihar Borno.
Har wala yau, a matsayin shi na shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso gabas, Gwamana Zulum ya bukaci gwamnatin tarayya ta ci gaba a yunkurin samar da tashar hasken wutar lantarki a Mambila da Dadin- Kowa a jihohin Taraba da Gombe, tare da shaidar da cewa matukar an kammala wadannan ayyuka guda biyu, za su taimaka wajen bunkasar ci gaba da tattalin arzikin yankin.
A nashi jawabin, ministan makamashi, Engr. Mamman ya bai wa Gwamnan tabbacin cewa duk da yanayin da ake ciki na kalubalen tsaro, aikin sake gyara wutar zai kammala a yan kwanakin nan.
A fannin bukatar samar da layukan wutar lantarki mai amfani da hasken rana, ministan ya shaida wa Zulum cewa a wannan shekara ma’aikatar ta sanya sunayen wasu garuruwan da za ta sanya wutar, wanda jihar Borno ta na daga ciki.
Bugu da kari, Daraktan ma’aikatar, Engr. Faruk Yabo Yusuf hadi da Manajan Daraktan kamfanin kula da raba wuta ta Nijeriya (TCN), Engr. Sule Ahmed Abdulaziz, duk sun bai wa Gwamna Zulum kwarin gwiwa dangane da gudanar da sabbin ayyukan samar da wutar a jihar Borno.
Wanda a karshe ministan, ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Zulum dangane da wannan ziyara tare da yaba masa bisa ga yadda yake gudanar da salon shugabancin al’umnar jihar Borno mai cike da dattaku, gaskiya da rikon amana: a fada a cika.