Ahmed Muh'd Danasabe" />

Matsalar Ruwan Sha A Lokoja Za Ta Zama Tarihi, Cewar Injiniya Abdulsalam

Injiniya Abdulsalam

Biyo bayan matsalar rashin ruwan sha da a yanzu ke addabar birnin Lokoja da kewayenta a yan kwanakin nan, lamarin data jefa mazauna birnin cikin halin yani yasu,har ya kai ga suna koka wa matuka gaya, janar manajan hukumar kula da samar da ruwan sha na jihar Kogi( Kogi State Water Board), Injiniya Sagir Abdulsalam ya bada tabbacin cewa da yardan Allah nan bada dade wa ba, matsalar karancin ruwan shan zai zama tarihi domin kuwa gwamnatin jihar tana nan tana bakin kokarinta wajen ganin ta kawo karshen matsalar.

Injiniya Sagir Abdulsalam ya bada tabbacin ne a yayin da yake tattauna wa da wakilin jaridar LEADERSHIP A yau a ranan Asabar data gabata, a garin Lokoja.

Janar manajan yace gwamnati mai ci a yanzu a jihar karkashin jagorancin Alhaji Yahaya Adoza Bello ta damu matuka gaya kuma tana sa ne game da irin halin da al’ummar birnin Lokoja da kewayenta suka tsinci kansu ciki biyo bayan karancin ruwan sha dake addabar birnin dama sauran sassa daban daban na jihar, inda ya kara da cewa a yanzu haka babban kalubalen dake gaban gwamnati shine yadda zata wadata jama’arta da abubuwan more rayuwa, ciki har da tsaftataccen ruwan sha.

Injiniya Sagir Abdulsalam ya kuma bayyana da cewa akwai wasu muhimman matsaloli da hukumar ke fuskanta wanda hakan ne ya haddasa karancin ruwan sha da birnin na Lokoja ke fuskanta,yana mai bada alwashin cewa nan bada dade wa ba lamarin zai kawo karshe.
Daga nan Injiniya Sagir Abdulsalam ya roki al’ummar birnin na Lokoja dasu kara hakuri a dai dai lokacin da hukumar ta samar da ruwan shan ke fadi tashi wajen ganin ta kawo karshen matsalar dake ciwa mazauna birnin na Lokoja da kewayenta tuwo a kwarya.

Wakilin LEADERSHIP A YAU wanda ya zazzaga birnin na Lokoja, ya nakalto cewa mazauna unguwanni daban daban dake birnin a yan kwanakin nan suna fuskantar matsanancin karancin ruwan sha, inda zaka ga magidanta maza da mata da kuma yara kanana dauke da kayayyakin dibar ruwa suna neman ruwan shan a jallo, duk da cewa birnin na Lokoja gari ce inda kogunan Neja da Binuwe suka hadu,wato( confluence of Riber Niger & Benue) a turance.

Exit mobile version