Matsalar Tsaro A Kebbi: Makiyayi Ya Kashe Sufetan Dansanda

A jiya, rahotanin da ke fitowa daga garin Kaoje a karamar hukumar Bagudo a Jihar Kebbi sun bayyana cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta samu nasarar cafke wani mutum da ake zargi da kashe babban jami’in ‘yan sanda mai mukamin insifeto, Umaru Dan ladi da ke aiki a ofishin rundunar na garin Kao’je.
Wata Majiya mai tushe da ta nemi a sakaye suna ta sheda wa jaridar LEADERSHIP A Yau juma’a cewa”wani mutun ne Mai suna Babuga Manu Kaura wanda kuma Bafulatani ne mai kiyon shanu a dajin garin kao’je ne ya kashe wani insifeto na rundunar ‘yan sandar da ke kao’je kan yi wa wani manomi barna a cikin gonarsa a jiya , daga nan ne manomin ya kai kara a ofishin ‘yan sanda da ke garin na kao’je a cikin karamar hukumar Bagudo sai aka umurci marigayi insifeto Umaru Danladi cewa ya je ya taho da Bafulatanin, bayan zuwansa gonar manomin wanda ba a bayyana sunan sa ba inda ya sanya Bafulatanin gaba domin zuwa ofishin na ‘yan sanda na garin na kao’je daga nan ne Bafulatanin Mai suna Babuga Manu Kaura ya zaro addarsa ya sari dan sadan har ya mutu”.
Haka kuma majiyar ta ci gaba da cewa “ bayan ya kashe dan sandan sai manoma a dajin na garin kao’je suka lura da cewa Bafulatanin ya sassara dan sandan da adda sai suka kama Bafulatanin tare da shanunsa a cikin gonar ta manomin da ya yi wa barna daga nan ne daya daga cikin manoman ne suka kira ofishin na ‘yan sanda na garin na kao’je domin kawo dauke a dajin”. Bayan ofishin na ‘yan sanda sun samu labarin abin da ya faru daga nan suka kai dauke domin tabbatar da cewa sun cafke Bafulatanin.
Bugu da kari majiyar ta cewa” ‘ yan sandan da suka kawo dauke daga garin na ka’oje sun kama shi tare da shanunsa a cikin gonar amma kuma shi insifeto Umaru danladi ya riga mu gidan gaskiya”.
Domin samun tabbacin aukuwar lamarin jaridar LEADERSHIP A Yau juma’a ta nemi jin ta bakin rundunar ‘yan sandan ta jihar Kebbi kan kisan insifeto Umar Danladi da ke a ofishin na garin ka’oje inda Mai magana da yawun rundunar PPRO DSP Mustapha Suleiman” ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Birnin-kebbi a jiya”. Ya ci gaba da cewa “ rundunar ta cafke Babuga Manu Kaura kan kashe jami’in rundunar watau insifeto Umaru Danladi inda Bafulatanin anan take ya amsa zargin da ake yimasa kan kisan dansanda”.
Daga karshe ya ce rundunar za ta gabatar da shi a gabata kotu da laifin kisan dan sanda domin yimasa hukuncin da doka ta tanadar kan kashe mutun “.

Exit mobile version