Daga Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko,
An bayyana rungumar addu’oi dare da rana da daina saba wa Allah da kuma hadin shugabannin da suke arewacin Nijeriya cewar su ne manyan abubuwan da za su dawo da zaman lafiyar da al’ummar arewa suka rasa a yau, ba aiwatar da wasu abubuwa na daban ba.
Babban Limamin Tudun Wadan Zazzau Shekh Malan Dan Tine ya bayyana haka a lokacin day a zanta da wakilinmu kan matsalolin tsaro da ka iya cewar, matsalar ta na neman ta zama kadangaren bakin tulu ga gwamnatocin da suke jan ragamar Nijeriya a yau.
Babban abin da ya samar da wannan matsala ta tsaro, kamar yadda shehin Malamin ya ce su na da yawa, amma kamar yadda ya ce yadda al’umma babu jin kunyar wanda ya halicce su, sai sabon Allah al’umma suka runguma da hannu biyu, ba tare da tunanin a kwai ranar kin dillanci.
Shehin malamin ya ci gaba da cewar, matukar al’umm suka runbumi badala dare da rana, abin za su fuskanta shi ne matsalolin tashe – tashen hamkali da suka hada da rashin tsaro da garkuwa da muytane da sauran matsalloli ma su yawan gaske da suka dabaibaye al’umma a wannan lokaci da mu ke ciki.
Da kuma Shekh Dan Tine ya juya ga al’ummar kasa ya bukace su da su kasance ma su yi wa kasa addu’o’I tare da shugabannin da suke jagorantar fallen gwamnati uku, in an yi haka, babu ko shakka, shugabannin za su sami saukin fuskantar ayyukan da aka dora ma su, na shugabanci ko kuma na wakilcin al’umma, tun daga kananan hukumomi ya zuwa jihad a kuma tarayya.
Domin kawo karshen matsalolin tsaron da su ke addabar al’ummar arewacin Nijeriya kuwa, babban limamin Tudun Wadan Zariya, ya tunatar da su lokaci ya yi da za su sami fuskantar matsalolin tsaro a duk rana matsalolin sai kara ta’azzara su ke yi, kamar yadda ya ce zaman ‘yan marina da suke yi a halin yanzu, babbar matsala ce.