Daga Shehu Yahaya
Biyo bayan hare-hare da garkuwa da mutane da ‘yan bindiga suka kaddamar a ‘yan kwanakin nan a wasu yankuna a jihar Kaduna, al’ummar jihar Sun bukaci gwamnati da ta kawo mu su dauki domin kare rayukansu da dukiyoyinsu Kamar yadda gwamnatin tayi alkawari.
Kananan hukumomin Igabi da Giwa da Chikun da kuma Birnin Gwari suna daga cikin yankunan da yanzu matsalar rashin tsaro yayiwa katutu, lamarin da sanya wasu mutanan barin matsugunnansu.
Garuruwan Marabar Jo’s da Birinin Hero da Jaji da Gwaro Da Barkono dake cikin karamar hukumar Igabi suna daga cikin yankunan da matsalar ‘yan bindaga tayiwa katutu Kamar yadda mazauna garin suka shaida inda suka ce da zarar karfe shida na yamma tayi babu mai iya fita ko zirga-zirga a yankin.
A farkon wannan makon mazauna garin Marabar Jos da Birnin Yero dake cikin karamar hukumar igabi. Sun kwana cikin zullumi bisa samame da maharan suka kawo garin inda sukace akalla mahara Sama da Guda 100 akan mashina suka shigo garin.
A wata ziyarar da wakilinmu ya Kai a kananan hukumomin Birnin Gari da Giwa da Igabi da kuma Chikun ya zanta da mutanan yankunan akan matsalar rashin tsaron da ya addabesu inda suka bukaci gwamnatin jihar data kawo musu dauki domin ceto rayuwarsu daga hannun mahara.
Alhaji Garba Gumbo Randagi, shi ne shugaban karamar hukumar Birnin Gwari, ya bayyana cewa Sun dauki matakai masu yawa wajen tabbatar da magance matsala rashin tsaro a karamar hukumar inda yace matsalace da bazata magantu lokaci daya Ba.
“Ina mai tabbatar maka da cewa karamar hukumar Birnin Gwari ta himmatu wajen daukar matakai akan wannan matsala, Kamar yadda nace Ba matsala bace da rana Guda zamu magance amma dai muna iya bakin kokarinmu. Kaga yanzu Mun samar da ofisoshin jami’an tsaro a yankunan da suke fama da matsalar domin zaman kota kwana haka kuma muna samar da kayan Aiki ga jami’an tsaro, akwai matakai da yawa da muke dauka Wanda bazan iya fadansu a kafafen yada labarai ba.
“Domin magance matsalar ni da sakataran karamar hukumar da wasu malaman mu da hakimai Mun zauna da shugabannin wadannan maharan a wani daji dake cikin karamar hukumar inda muka bayyana musu damuwarmu akan yadda Birnin Gwari tayi kaurin suna wajen kashe -kashe na ta’addanci, Sun fada mana dalilinsu da kuma zayyana mana sharudda muddin muna son a rage yawaitar hare-hare a yankunan . Mun dauki matakan da suka gindaya mana, alhamdulillahi! Yanzu an samu saukin Kai hare-hare a Birnin Gwari,” in ji shi.
Usman Yunusa, mazaunin garin Rigachikun dake cikin karamar hukumar Igabi, shima ya bayyana takaicinsa dangane da yadda suka bar gidajensu domin kaucewa fadawa hannun masu garkuwa da mutane.
“Abin takaici gwamnatin jihar ta San da wannan matsala amma babu wani mataki da aka dauka. Mu dai yanzu muna bukatar dauki daga gwamnati na kare rayukanmu da dukiyoyinmu.”
A wata hira da gidan talabijin mallakar gwamnatin jihar Kaduna Wato KSTB tayi da kwamishinan ma’aikatar tsaro da lamuran cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar zata ci gaba da daukar matakan da suka kamata wajen yaki da muyagun mutane a fadin jihar yana mai cewa yanzu haka suna Aiki babu dare babu rana wajen bankado duk wani masu aikata laifuka a fadin jihar.
Samuel Aruwan, ya bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu a cewarsa, gwamnatin jihar tana baki kokarinta wajen magance matsalar tsaro a fadin jihar baki daya.
A kan hakan ya bukaci daukacin al’ummar jihar da su ci gaba da basu goyon baya ta hanyar sanar da musu da rahoto akan duk wani Wanda basu aminta dashi Ba ga jami’an tsaro Wanda hakan zai taimakawa kokarin su na dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar baki daya.
Rahotanni Sun tabbatar da cewa a yankuna da yawa na kananan hukumomin Igabi da Chikun da Giwa wadanda da zarar karfe shida na yamma tayi babu shiga babu fita har sai kuma gobe da da safe zuwa karfe gama domin kaucewa shiga komar mahara da ‘masu garkuwa da mutane.
Hatta wasu unguwanni da ke cikin kwaryar jihar suma haka ake zaman zullumi da zarar dare ya yi.