Connect with us

LABARAI

Matsalar Tsaro: An Yi Addu’o’i Na Musamman A kananan Hukumomin Yankin Funtuwa

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin gwamna Alhaji Aminu Bello Masari ta bada umurnin yin addu’oin samun zaman lafiya a dukkan fadin jihar.
An fara addu’oin da misalin karfe 10 na safe zuwa sha biyu na ranar Litinin din nan da ta gabata.
Wakilinmu ya ziyarci kananan hukumomin Danja, Bakori da Funtuwa da karamar hukumar Dandume duka kowace karamar hukuma an dauki malaman addinin guda 100, 50 daga kungiyar Izala, 50 daga kungiyar Darika don gudanar da addu’oin na musamman a yankin.
A karamar hukumar Danja shugaban riko na karamar hukumar Alhaji Hamza Umar Sabuwar kasa ya yi kira ga sauran al’umma da suji tsoron Allah a duk inda suke kuma a guji sabon Allaha maida hankali wajen karatun Alkur’ani mai girma, Shugaban riko na karamar hukumar Danja Alhaji Hamza ya ci gaba da cewar mutane su guji yada jita-jita a duk inda suke kuma mutane mu ji tsoron Allah ya gode ma mai girma Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari wajen tunanin shi na yin addu’oi don samun zaman lafiya da karuwar arziki a jihar da ma kasa baki daya, daya daga ciikin wanda ya wakilci gwamnan jihar Alhaji Bishir Ruwan Godiya mai ba gwamna shwara a kan ilimi mai zurfi a nashi jawabin tun farko ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina su mike tsaye wajen gudanar da addu’oi a ko da yaushe don samun tabbataccen zaman lafiya da karuwar arziki.
Dakta Bishir Ruwan Godiya wanda shima ya yi karatun Alkur’ani mai girma a karamar hukumar Danja.
A nasu jawabin daban daban shuwagabannin riko na kananan hukumomin Funtuwa da Dandume da na karamar hukumar Bakori Alhaji Abba Magaji Ingawa ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar Bakori da su cigaba da bautar Allah kamar yadda ya dace kuma su kara ba gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari goyon baya, shugaban riko na karamar hukumar mulki ta Funtuwa Alhaji Umar Tsoho Mustapha Kankara da na karamar hukumar Dandume Alhaji Ahmed Idris Mashi dukkan su sunyi kira ga jama’ar kananan hukumominsu da su cigaba da ba gwamnatin jihar Katsina goyon baya da kira ga dukkan Malaman addinai na kananan hukumomin da suci gaba da yin karatun Alkur’ani hade da yin addi’oin samun zaman lafiya da kuma hana yaduwar cutar korona birus a cikin al’umma kuma sun gode ma gwamnatin jihar Katsina wajen bayar da umurnin don yin addu’oi na musamman, Mutane su guji yawaita sabon Allah SWA kuma a cigaba da fadakar da kawunan jama’a wajen cudanya da jama’a kuma a kiyaye dokokin da masana kiwon lafiya keyi wajen hana yaduwar wannan cuta mai ci kamar wutar daji.
Daga karshe dukkan hakiman kananan hukumomin Bakori, Danja, Dandume, da na karamar hukumar Funtuwa Alhaji Sambo Idris Sambo dana Danja sarkin kudun Katsina Alhaji Bature da na Dandume katukan Katsina wanda Magajin Jiruwa ya wakilce shi da hakimin Bakori makaman Katsina Alhaji Sule Idris Sule sun gode ma gwamnan jihar da mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.
Advertisement

labarai