Connect with us

MANYAN LABARAI

Matsalar Tsaro: Barazana Kurum Buhari Ke Yi – Dattawan Arewa

Published

on

  • An Kai ’Yan Arewa Bango Fa, Cewarsu

An bayyana cewa, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari barazana kawai ya ke yi kan batun matsalar tsaro, wacce ta dabaibaye yankin Arewa, amma a zahirance ba ya daukar matakan da su ka dace, don shawo kan matsalar dungurugum.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar Dattawan Arewa (Northern Elders Forum, NEF) mai dauke da sa hannun jagoranta, Farfesa Ango Abdullahi, a karshen makon nan.

Sanarwar ta ce, an san mutanen yankin Arewa a matsayin al’umma mai yakana, hakuri da juriya, to amma Gwamnatin Nijeriya a karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta na yin amfani da wannan dabi’a tasu wajen yin shakulaton bangaro da halin matsin da su ka tsinci kansu, musamman na tabarbarewar tsaro, inda shugaban ya kan yi barazanar bayar da umarnin dakile matsalar ne kawai ba tare da daukar matakan da su ka dace ba.

Sanarwar ta ce, “Northern Elders Forum (NEF) ta damu da halin matsalar tsaro da a ke cigaba da samu a cikin al’ummomi da kadarorin mutanen Arewa. Irin yadda a kwanan nan a ke cigaba da samun hare-hare daga ’yan bindiga da masu garkuwa, hakan ya san ba a da zabin da ya wuce a ce yanzu sai yadda wadannan ’yan ta’adda su ka yi da su. Daga dukkan alamu gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnoni ba sa yin katabus wajen kare al’ummar Arewa, wanda hakan ne nauyin da kundin tsarin mulkin su ka rantse da shi ya dora mu su.

“Al’amarin kullum sake tabarbarewa ya ke yi. ’Yan bindigar sun gano gazawar kyakkyawar aniyar siyasa da kuma kumajin gwamnati, inda su ke yin amfani da wannan dama wajen gallazawa al’ummomi da daidaikun mutane. Ba za a ce an zuzuta ba, idan a ka ce, al’ummar Arewa ba su taba fuskantar matsananciyar matsalar tsaro irin ta wannan lokaci ba, inda a ke kai mu su hari, yi mu su fyade, garkuwa da su, kone kauyukansu da sace shanunsu, inda shi kuma gasorogon Shugaba Buhari ya kare da yin barazana da daukar alkawuran da ba zai iya cikawa ba.

“Halin da al’ummominmu ke ciki tun daga Kogi zuwa Borno da Sokoto har zuwa Taraba su ke ciki ba abin a cigaba da dauke kai a kai ba ne. Don haka a matsayin wannan kungiya mai sanin yakamata, kungiyar ta shiga sahun miliyoyin masu yin addu’o’i da kuma bai wa dukkan hukumomi shawara da karfafa mu su gwiwa wajen sauke nauyin da ke kansu na al’ummarmu.

“Lokaci ne da a yanzu za mu iya cewa, tura ta kai bango. An san mutanenmu da mutunta hukumomi, amma dole ne gwamnatoci su sani cewa, an kai ’yan Arewa bango fa.

“Mu na sane da cewa, wasu ’yan kasar su na nan su na duba yiwuwar gudanar da zanga-zanagar lumana, wacce su na da hakkin yin hakan a kundin tsarin mulkin kasa, don su janyo hankalin Shugaba Buhari da dukkan hukumomin da ke da hakki kan halin da al’ummar Arewa ke ciki. Amma kungiyar nan ta na jan hankalin dukkan ’yan kasa da su nuna halayya ta zaman lafiya da hali nagari, sannan su kuma hukumomi su mutunta ’yancin ’yan kasa na bayyana ra’ayi cikin lumana.

“Haka nan, kungiyar ta na yin tuntuba da wasu kungiyoyin da su ke da akida iri guda, don hada hannu waje guda, domin neman daukar matakan da su ka dace wajen nema ma na sauki kan halin da mu ke ciki na kashe mu da a ke yi da kuncin rayuwa da a ke jefa mu ba tare da mun ji ko mun gani ba a Arewa.

“Kungiyar ta na kuma tunatar da Shugaba Buhari cewa, samar da tsaro da walwala ga ’yan kasa su ne ginshikin nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa shugabanni a kowane mataki. Don haka halin da Arewa ke ciki a yanzu ya na nuni da cewa, mulkin Shugaba Buhari ya yi matukar gaza cimma su. Wannan ba abin amincewa ba ne. Mu ne neman a gyara halin matsalar tsaron da Arewa ke ciki nan take. Mun gaji da gafara-sa ba tare da mun ga tsaro ba, wanda masu aikata laifin ma dariya su ke yi a kai, kuma sauran ’yan uwanmu ’yan kasar su na kallon lamarin a matsayin gazawa ta zahiri. Tura dai ta kai bango.”

 
Advertisement

labarai